Gwamnatin Tinubu ta ƙaddamar da shirin cibiyoyin ƙera kayan gine-gine

Spread the love


Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da shirin kafa cibiyoyin ƙera kayayyakin gine-gine da ake amfani da su wajen gine-gine a shiyyoyi shida na Nijeriya.

Za a kafa cibiyar shiyyar Kudu maso yamma a jihar Ogun, kudu maso gabas a jihar Abia, kudu maso kudu a Warri ko Asaba dake jihar Delta, Arewa ta Tsakiya a Ajaokuta dake jihar Kogi, Arewa Maso Yamma a Jihar Kano, sai kuma Arewa maso gabas a jihar Gombe.

Wannan cibiyoyi zasu samar da ayyukan yi ga dubban matasa a faɗin ƙasar, a lokaci guda kuma zasu rage tsadar kayayyakin gine-gine da ake shigo da su Najeriya. Haka zalika za a samu damar ƙera kayayyakin gine-gine a nan cikin gida Nijeriya da kuma kara haɓaka tattalin arziƙin Ƙasar.

Ababen da za a samar a cibiyoyin sun haɗa da Kwanon Rufi, Silin, tiles da ƙofofi.

By ukarofi