Ambaliya ta yi ajalin jami’in tsaro da matashi a Yobe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mamakon ruwan sama da aka zabga a sassan Damaturu, babban birnin jihar Yobe, ya haddasa ambaliyar da ta yi sanadiyyar rasuwar mutum biyu.

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) ta tabbatar da faruwar al’amarin a wata takarda da ta fitar a ranar Talata.

Ta ce, waɗanda iftila’in ya yi ajalin nasu sune wani jami’in tsaro mai suna Mallam Matari da wani matashi ɗan kimanin shekaru 18, Abba Kyari, waɗanda ambaliya ta halakar a yankin Pompmari.

A cewar hukumar, ambaliyar ta auku ne a Malari, Pompomari da kuma wasu yankunan kewayensu bayan wani ruwan sama da aka yi a safiyar ranar Litinin.

SEMA ta bayyana cewa, tawagar bincike da ceto na ofishinta da haɗin-gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta jihar ne suka gaggauta kai ɗauki wajen da abin ya faru, inda suka samo mutane biyu a mace.

Daga lokacin ne aka garzaya da gawarwakinsu zuwa sashen gaggawa na Babban Asibitin Janar Sani Abacha da ke Damaturu.

Kazalika, hukumar ta yi kira ga mazauna musamman waɗanda suke wuraren da ke fuskantar barazanar ambaliya, da su riƙa kulawa a yayin da ake ruwan sama da kuma ƙaurace wa tafiya, wasa ko ninƙaya a hanyoyin ruwa.

Har illa yau, ta gargaɗi iyaye da su hana yaransu zuwa rafuka, koguna da dukkan wasu wuraren ruwa, tana mai cewa a yanzu ana hutu a makarantu don haka yara su riƙa zama a gida yayin da ake ruwan sama shi ya fi dacewa.

By Babaji

Leave a Reply