Gwamnan Kaduna ya karɓi baƙuncin matar marigayi Edwin Achi da mijin Ummulkhairi da aka halaka a Maraba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Talata Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya karɓi baƙuncin mijin matar nan mai suna Ummulkhairi Aliyu da aka halaka a yankin Maraban Jos, wato Malam Usman Aliyu da kuma matar marigayi Ven. Edwin Achi, Misis Sarah Achi.

Uba Sani ya karɓi baƙuncin nasu ne a gidan gwamnatin jihar a lokacin da suke je nuna godiyarsu a gare shi bisa tallafa musu.

Yayin da suka samu rakiyar babban faston Kaduna, Reberen Timothy Yahaya da Sheikh Haliru Maraya, mutane biyun sun yi godiya ga gwamnan bisa cika alƙawuran da ya musu na samar musu da gidaje, tallafin kuɗi da kuma tallafin karatu ga ‘ya’yansu.

Haka kuma, sun yaba da tsarin jagorancinsa a jihar na damawa da kowane ɓangaren al’ummar jihar da kuma shugabancin fifita lamuran al’umma kai tsaye.

A nasa jawabin, Uba Sani ya ce hakan wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsa wajen faɗaɗa shirinta na tallafa wa al’umma, wanda a ƙarƙashinsa an samar wa mutanen da ayyukan ‘yan bindiga ya shafa a jihar rukunin gidaje guda 100.

Kazalika, ya jaddada aniyarsa ta ƙoƙarin dawo da kyawawan fata da kare mutuncin iyalan da ta’addanci ya shafa a sassan jihar.

By Babaji

Leave a Reply