Daga MUKHTAR YAKUBU
Kasuwanci ana nufin saye da sayarwa. Duk wani aikin da mutum zai yi amfani da basirar sa ko kuma abin da ya koya daga wajen wani ko a makaranta ya aiwatar da shi domin neman kuɗi, shi ake cewa wa sana’a a Hausance. Ma’ana duk wata sana’a ta hannu kamar dinki, saka, kitso,kanikanci, tuki da makamantan su, su ake kira sana’ar hannu.
Ita dai kalmar karuwanci, kalma ce da bahuashe ya aro ta daga wajen Babarbare, a kalmar da suke cewa Karuwa, ma’ana mai yawun iska ko kuma iska, inda shi kuma Malam Bahaushe ya mayar da kalmar karuwanci, a nufinsa ‘yar iska. Kuma wannan ne yake kira duk wata mace mai yawon ta zubar ko kuma mace mai zaman kanta.
Sai dai kuma kalmar karuwancin da bahaushe yake da ita ta asli ita ce kilaki.
Duk inda bahaushe ya ambaci mace da sunan kilaki yana nufin matar banza kenan mai zaman karuwanci ko kuma mai zaman kanta.
Idan muka haɗa waɗannan kalmomin guda biyu da karuwanci da kuma sana’a za mu ga cewa a yanzu mata da dama sun mayar da karuwanci a matsayin sana’ar da suke alfahari da ita kuma suke riƙe kansu wani lokutan ma har ma da ‘yan uwansu, iyaye da ma ‘ya’yansu idan suna da su.
Duk wata macen da take bada jikinta, farjinta domin a kwanta da ita a bata kudi, sunanta karuwa a hausance. Kai ko da ba a kwanciyar da Ita in dai tana amfani da siffar jikin ta wajen jan hankalin maza tana samun kuɗi to wannan karuwanci ne.
Karuwa da mazinaciya suna da bambanci a hausa.
Ita mazinaciya tana yin zinar ne ko dai saboda sha’awa ko kuma saboda soyayya amma ba domin a bata kuɗi ba.
Sai dai kuma yadda ‘yan matanmu na arewancin suke tafiyar da sana’arsu na karuwancin ya bambanta da na matan kudanci, akasarin ‘yan matan kudancin su ne ake ganinsu suna sana’ar karuwanci na zaman kujera, wanda yana da matuƙar wahala ka ga macen Arewa ta kama ɗaki idan yamma ta yi ta samu kujera ta zauna a bakin ƙofa ta na jiran abokin zinanta ko mu ce abokin sana’ar nata ya zo. Wannan an fi ganin matan kudancin da irin wannan karuwancin.
A binciken dana gudanar na gano cewa karuwai sun kasu kashi- kashi da dama, kuma kowacce da irin yadda take tafiyar da nata karuwanci da kuma inda tafi maida hankali wajen samo abokan kasuwancin nata.
Haka kuma da akwai karuwan gida wanda akasarinsu a gidajnen iyayensu suke ko gaban magabantasu amma suke fita waje su je su yi baƙar sana’ar tasu kuma su dawo gida ba tare da sun fuskanci wata tsangwama daga ‘yan unguwa ko kuma magabatan nasu ba. Kuma yanzu abin da ya fi yaɗuwa kenan musamman a manyan birane na Arewa.
Akasarin irin waɗannan matan kuwa an fi samun su a cikin zaurawa da ‘yan boko da kuma irin kangaranrun ‘yan matan nan da ba su taɓa aure ba.
Akwai yaran da idan yamma ta yi za su fita daga gidan iyayen su. Ba su sanin inda suka nufa sai sun je wajen haɗuwa, ko wajen shan shayi ko wajen masu Indomie. A nan za su haɗu da abokan harkar su, su saya musu abinci su ɗauke su a abin hawa ko dai su yi lalata da su a cikin motar ko kuma su kai su wani keɓantaccen wajen.
Idan su gama ko su mayar da su wajen ko su kawo su bakin titi su tare musu abin hawa su kama gaban su.
Wasu matan kuma suna bin otal ne a nan su ke samun abokan harkar su, idan sun samu wanda zai kwana da su, su kwana da safe su koma gida. Idan kuma na lokaci ne sai su gama komai dare su kama gaban su.
Akwai kuma masu kama ɗaki, waɗannan manya ne suna da kwastomomi, wasu ma ajiye su aka yi akwai mai biya musu daɗin, don haka koda yaushe suna cikin otal, idan wanda ya ajiye su yana nan suna tare da shi idan kuma ba ya gari su nemi wasu ko a neme su. Irin waɗannan sai ka ga mace ta shafe sama da shekara guda a cikin otal.
Mafiyawan karuwan da na zanta da su, sun yi mini bayani ne a kan alfanun da kuma rashin alfanun sana’ar tasu, inda wasu suka nuna yadda sana’ar ta ba su damar mallakar abubuwan alatu na rayuwar duniya, amma kuma daga ƙarshe suka yi nadama, wasu kuma har yanzu suna cikin walwalarsu, wasu kuwa ko zanin ɗaurawa ba su da shi bare kuma abincin da za su ci na yau da gobe.
Halima ( Na boye sunan ta) yarinya ce mai kimanin shekaru 27 da haihuwa kyakkyawa ce a yawon bincikena na tsinto ta a gidan wata tsohuwar karuwa wacce ta haɗa ni da akasarin ‘yan mata karuwan da na yi hira da su. Inda Halima wanda ba sunanta na asali ba ne ta tabbatar mini da irin bakar wahalar da suke fuskanta a wannan sana’ar tasu ta karuwanci inda ta soma da bani labari kamar haka.
” A gaskiya babu wani daɗi a wannan sana’ar sai baƙar wahala tun da abin da ka tambayeni kenan. Ni dai na fi zuwa inda ake kidan goge ko garaya ne, domin nan muke samun abokanen sana’ar mu, wata rana mu yi dace wani lokacin kuma na sigari ma da kyar za ki dawo gida shi, gashi kuma kusan kullum sai mun biya kuɗin ɗaki kuma sai mun bai wa uwargidanmu kuɗi.”
Za mu ci gaba mako mai zuwa.
