
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta dakatar da asusun bankin gwamnatin Jihar Osun na Bankin ‘First Bank’, kwanaki goma kafin zaɓen gwamnan jihar.
A cewar wasu takardu da jaridar Vanguard ta samo, asusun, wanda da shi ake biyan ma’aikata albashi, an sanya shi a tsarin “Post No Debit”, wato yadda ba za a iya fitar da wani kuɗi a ciki ba.
Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan Gwamna Ademola Adeleke na jihar ya zargi EFCC da shirin dakatar da asusun bankunan da gwamnatin ta mallaka da na wasu manyan jami’an gwamnati gabanin zaɓen, wanda za a gudanar a ranar 15 ga watan Agusta.
Da yake tsokaci kan al’amarin, Kwamishinan Yaɗa Labaran jihar, Kolapo Alimi ya bayyana matakin a matsayin yunƙurin hargitsa harkokin gwamnatin yayin tunkarar zaɓen.
Gwamnan Adeleke ya ce, babu wata doka da ta hukunta dakatar da asusun jihar, inda ya tirje akan cewa EFCC ba ta da ikon ɗaukar matakin akan gwamnatin jihar.
Wata majiya da ke da kusanci da gwamnatin jihar ta ta nemi a sakaye sunanta, ta tabbatar da cewa an riga an dakatar da asusun.
A yayin aikin haɗa wannan rahoto, hukumar EFCC ba ta fitar da wani bayani ba a hukumance kan batun, lamarin da ya sa ba a gano ainihin abin da ya sa ta ɗauki matakin ba.
