‘Yan sanda sun kama mutum biyu da ke da hannu wajen sace sojoji a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta sanar da kama waɗansu mutane biyu da ke da hannu wajen sace sababbin sojoji a kan hanyar Anka zuwa Bukkuyum da ke jihar Zamfara yayin da su ke kan hanyar su bayan kammala karɓar horo daga makarantar horon ƙananan sojoji (Depot) Zaria.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi Sufurtandan ƴan sanda Bashir Usman ne ya sanar da haka ga manema labarai a garin Birnin Kebbi ranar talatar nan.

Ya ce waɗanda aka kama sun haɗa da Abubakar Mallam Abubakar Gargam Bagega ƙaramar hukumar mulki ta Anka jihar Zamfara, Usman Muhammadu Ajera daga garin Ilorin a jihar Kwara.
Ya ce kama waɗannan mutanen ya biyo bayan samun bayanan sirri inda rundunar ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta bi sawun su kuma ta sami nasarar kama su.

Ya ƙara da cewa sojojin da aka sace tuni sun sami kan su kuma ana nan ana tatsar bayanai daga ɓarayin a sashen bincike na rundunar a jihar Kebbi kuma da zarar aka kammala za a ɗauki mataki na gaba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Umar Haɗejia ya yaba wa waɗannan jami’an ƴan sanda bisa ga irin ƙoƙari da ƙwarewar da suka nuna.

By ukarofi

Leave a Reply