
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Cibiyar shirya jarrabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta fitar da sakamakon jarrabawar shaidar WASSCE, inda ɗalibai 1,200,514 suka yi nasara a aƙalla darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.
WAEC ta sanar da haka a yau Laraba ta sahihin shafinta na kafar X, inda ta umarci ɗalibai da su duba sakamakonsu ta yanar gizo.
Da yake sanar da labarin fitar da sakamakon a Babban Ofishin WAEC na Nijeriya a Legas, Dakta Amos Josiah Dangut, ya ce kimamin ɗaliban ƙasar miliyan 1.2 ne suka wakilci kaso 61.54 na adadin waɗanda da suka rubuta jarrabawar, lamarin da ke nuna an samu faɗuwar kaso 1.42 na ɗaliban 2025.
A cewar WAEC, ɗalibai 1,959,668 daga makarantu 24,207 a Nijeriya, Jamhuriyar Benin, Côte d’Ivoire da Equatorial Guinea ne suka yi rajistar jarrabawar yayin da 1,950,726 suka yi zaman rubutawa.
Ta ce, ɗalibai 1,687,378 da ke wakiltar kaso 86.50 sun samu kiredit biyar ba tare da la’akari ko sun yi nasara a Turanci da Lissafi ko ba su yi ba.
Dalla-dallar bayanan ɗaliban da suka yi nasara ta nuna cewa, maza guda 558,883 ne (wato kaso 28.65) da mata 641,631 (kaso 32.89) suka samu kiredit biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.
Jimillar maza 953,459 da mata 997,267 ne suka rubuta jarrabawar.
Sannan, WAEC ta ce ta kammala fitar da sakamakon ɗalibai 1,834,695, wanda ke wakiltar kaso 94.05, yayin da take cigaba da aiki kan sakamakon na guda 116,031.
Game da ayyukan satar jarrabawa, WAEC ta ce ta riƙe sakamakon na ɗaliba 167,486, wanda ke wakiltar kaso 8.59 na jimillar waɗanda suka rubuta jarrabawar.
An gudanar da jarrabawar ne a tsarin amfani da takardu da kuma kwamfuta, inda makarantu da dama suka ɗauki tsarin amfani da kwamfuta wajen gudanar da jarrabawar sama da a shekarun baya.
A yanzu dai ɗalibai za su iya ziyartar sahihin shafin WAEC domin duba sakamakon jarrabawar tasu.
