Gwamnatin Katsina za ta raba Naira biliyan huɗu ga gundumomi 361

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya amince da fitar da Naira biliyan huɗu domin aiwatar da kashi na biyu na shirin cigaban Amal’umma (CDP) a dukkan gundumomi 361 na jihar, inda kowace gunduma za ta karɓi Naira miliyan 10 domin gudanar da ayyukan da al’umma suka fi buƙata.

A sanarwar bayan taron Majalisar zartaswa da jami’in hulɗa da jama’a na gwamna, Muhammadu Kaula ya sanya wa hannu, majalisar zartarwa ta Jiha ta amince da:
bayar da kuɗin haɗin gwiwa na shirin Nigeria for Women Project domin ƙarfafa tattalin arzikin mata.

Majalisar ta amince da samar da kayan ICT na zamani a makarantun model da ke Jiƙamshi da Dumurkul da
fitar da rahoton BERAP na 2025 domin inganta harkokin kasuwanci da jawo masu zuba jari.

Zaman majalisar da ya gudana ƙarkashin jagorancin Gwamna Dikko Raɗɗa, ta amince da sayo sinadaran tace ruwa da tura motocin ɗaukar ruwa domin tabbatar da ci gaba da samar da ruwan sha yayin gyaran cibiyoyin samar da ruwa.

Waɗannan matakai na nuna ƙudirin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa wajen bunƙasa cigaban al’umma, ƙarfafa mata, inganta ilimi, haɓaka tattalin arziki da tabbatar da wadataccen ruwan sha ga al’ummar Jihar Katsina,”Kaula ya ce.

By ukarofi

Leave a Reply