Gwamna Raɗɗa ya rantsar da sabbin manyan sakatarori

Spread the love

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya rantsar da sabbin manyan sakatarori (Permanent Secretaries) guda huɗu da suka haɗa da Malam Abdu Usman, Dakta Sani Suleiman, Dakta Shamsuddeen Yahaya Suleiman, da Dakta Hussaini Hamisu Yanduna.

Da yake jawabi bayan rantsarwar Gwamna Raɗɗa ya ce wannan muƙamin nasu ya tabbata ne bisa cancanta, ƙwarewa da jajircewa, ba tare da la’akari da alaƙa ko sanayya ba.

Ya buƙace su da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, riƙon amana da adalci domin inganta ayyukan gwamnati da hidima ga al’ummar jihar.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da adalci wajen ba da damar ci gaban ma’aikata, tare da ƙarfafa manyan jami’an gwamnati su riƙa horas da matasa domin samar da ƙwararrun ma’aikatan da za su ci gaba da inganta aikin gwamnati a Jihar Katsina.

By ukarofi

Leave a Reply