Jami’ar Bayero ta haramta caza motoci da baburan laturoni a harabarta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’ar Bayero da ke Kano ta hana caza babura da motoci masu amfani da wutar lantarki na masu zaman kansu acikin harabarta.

Jami’ar ta sanar da haka ne a wata sanarwa da ta fitar wa manema labarai ta hannu Daraktanta na kula da Harkokin Al’umma, Lamara Garba, ranar Talata.

A cewar sanarwar, hukumar gudanarwar jami’ar ta lura cewa ana amfani da lantarkin jami’ar wajen caza babura da wasu ababen hawa na lantarki yadda aka ga dama, lamarin da ya haifar da ƙarin kuɗin wuta da take biya da ɗora mata nauyin kuɗaɗen da suka zama wajibi ta biya.

Ta bayyana cewa, a daidai lokacin da take ƙoƙarin gudanar da abin da ta mallaka, cigaba da caza ire-iren ababen hawan na haifar wa jami’ar tsaiko, don haka ta ɗauki matakin haramtawar.

Akan haka ne ta shawarci dukkan ma’aikata, ɗalibai da masu amfani da babur wajen yin sana’ar acaɓa da su ƙaurace wa caza ababen hawan nasu da lantarkin makaranta, tana mai gargaɗin hukunta dukkan wanda aka samu da hannu a saɓa wa dokar.

By Babaji

Leave a Reply