Sojoji sun amshi mulkin Bangladesh

Spread the love

Sojoji sun ƙarbi mulkin Bangladesh bayan arcewar tsohuwar shugabar ƙasar Sheik Hasina. Babban hafsan sojojin ƙasar, Janar Waker-us-Zaman shine ya bayyana haka yayin da yake bada tabbacin za su kafa gwamnatin riƙon ƙwarya domin daidai al’amuran ƙasar.

Janar Zaman ya bada wannan tabbacin ne a wata sanarwa da yayi wa ƴan ƙasar a talabijin.

Janar Zaman ya kasance ɗan uwa na nesa ga shugabar da tayi murabus, sannan ya ƙasance yayi aiki kawo zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasashen Liberia da Angola.

Daga ƙarshe ya roƙi ɗaliban ƙasar wanda su ne suka fara wannan zanga-zanga da su bada haɗin kai domin kawo canji mai ɗorewa a ƙasar baki ɗaya.

By ukarofi