
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa, a ranar 3 ga watan Satumba, 2026 ne za a miƙa wa Shugaba Bola Tinubu ƙudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi domin yin nazari a kansa.
Shugaban Ma’aikatan fadar, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana haka, inda ya ce an tsara aikin ne cikin makonni bakwai domin kammala tsarin doka da zai bayar da damar aiwatar da shirin ‘yan sandan jihohin.
Ya ce, bayan shugaban ƙasa ya duba kuma ya amince da ƙudirin, za a gudanar da aikin tuntuɓar al’umma kafin a sake gabatar da shi a gaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa domin cigaba da ayyukan kammala amincewa da shi.
An buƙaci masu ruwa da tsaki da sauran al’umma da su aika da takardun shawarwari (memoranda) ta shafin nationalpolicingbill.com, domin a tattara dukkan ra’ayoyin da za su taimaka wajen inganta kudirin kafin shugaban ƙasar ya yi nazari a kansa.
Ana sa ran wannan mataki zai bai wa gwamnati damar jin ra’ayoyin jama’a kan yadda za a tsara aikin ‘yan sandan, wanda ya daɗe yana janyo muhawara a faɗin ƙasar nan saboda tasirinsa ga tsaro da tsarin mulki.
Wannan shiri na daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayyar na inganta tsarin tsaro da bai wa jihohi damar taka rawar gani wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma musamman bisa la’akari da ayyukan ta’addanci da ke faruwa a sassan daban-daban na ƙasar.
