
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Sufeto-Janar na Rundunar ‘Yan sandan Nijeriya, Alhaji Sulaiman Abba, ya nanata aniyarsa ta neman zama sanata a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar adawa ta PDP daga Jihar Jigawa a yayin babban zaɓen shekarar 2027.
Sulaiman Abba ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a ranar Lahadi, inda ya ce har yanzu yana da muradin cigaba da hidimta wa al’umma ta hanyar riƙe muƙaman siyasa.
A cewarsa, rashin ba shi damar tsaya wa takara a jam’iyya mai mulki (APC) ya yi tasiri wajen ɗaukar matakin sauya sheƙarsa zuwa PDP domin dacewa da kyawawan manufofinsa na siyasa.
Tsohon sufeto-janar ɗin ya kuma ce, a matsayinsa na mai ilimi kuma ƙwararre ta fuskar jagoranci da kuma samun arziƙin lafiya da son shugabanci, ya ga dacewar shiga takarar tsaya wa kujerar sanata ta mazaɓar Jigawa ta Kudu maso Yamma.
A ranar 4 ga Yuli, 2026, ne Alhaji Sulaiman Abba ya sanar da ficewarsa daga APC tare da koma wa PDP a hukumance bayan shafe kusan shekera huɗu a jam’iyyar mai mulki a matsayin mamba kuma jigo daga Jihar Jigawa.
Alhaji Abba, wanda ɗan asalin Gundumar Ƙofar Fada ne na Ƙaramar Hukumar Gwaram ta jihar, shi ne wanda ya jagoranci zaɓen 2015 bisa ƙwarewa da biyayya ga ƙa’idojin aikin ɗan sanda wajen tabbatar da gaskiya da adalci, lamarin da ya kai ga samun nasarar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a babban zaɓen.
A watan Junairun 2027 ne za a gudanar da babban zaɓe a Nijeriya, inda jam’iyyar APC da sauran jam’iyyun siyasa da suka haɗa da ADC, NDC, PDP, SDP da sauransu za su fafata a matakai daban-daban tun daga kujerar shugaban ƙasa har zuwa sanatoci, gwamnoni, ‘yan majalisar wakilai da kuma kujerun majalisun dokokin jihohi a wani salo mai ɗaukar hankalin al’umma musamman bisa la’akari da halin rashin tsaro da matsin tattalin arziƙi da ‘yan ƙasa suke fuskanta.

