Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya amince da fitar da Naira miliyan 500 a matsayin gudunmawar gwamnatin jihar ga Child Nutrition Fund, domin ƙarfafa yaƙi da tamowa da inganta lafiyar yara.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da sabon shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Shafeeq Ur-Rehman, ya kai masa ziyarar girmamawa. Ya ce haɗin gwiwar gwamnati da UNICEF ya taimaka wajen rage matsalar tamowa, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da saka hannun jari a fannonin lafiya da ilimi.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ɗauki malamai sama da 9,000 aiki, tare da alƙawarin ware ƙarin Naira biliyan 1.2 a kasafin kuɗin 2027 domin tallafa wa shirye-shiryen inganta abinci mai gina jiki ga mata masu juna biyu da yara.
A nasa jawabin, Mista Shafeeq Ur-Rehman ya yaba wa gwamnatin Katsina kan nasarorin da ta samu a fannoni lafiya, ilimi, abinci mai gina jiki da tsaftar muhalli.
Ya bayyana cewa Katsina ita ce jiha ta biyu a Najeriya da ta samu matsayin Open Defecation Free (ODF), kuma jiha ta farko da ta ware Naira miliyan 270 domin gudanar da SMART Nutrition Survey, tare da tabbatar da cewa UNICEF za ta ci gaba da haɗa hannu da gwamnatin jihar.
