
Daga BEL A. BABAJI a Abuja
Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa, Amurka da Isra’ila sun amince su dakatar da ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Iran matuƙar aka cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu cikin gaggawa.
Trump ya ce, ya yanke wannan hukunci ne bayan tattaunawa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, da kuma tattaunawar da Iram ɗin ta yi da Saudiyya, Pakistan da Turkiyya domin rage tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Saidai Iran ta musanta iƙirarin cewa ta roƙi Amurka ta dakatar da hare-hare, tana mai cewa kalaman na Trump ba gaskiya ba ne, tare da jaddada cewa dakarunta suna nan acikin shirin ko-ta-kwana kan abin da ka iya faruwa a nan gaba.
A cewar Shugaban Amurkan, duk wata yarjejeniya wajibi ne ta haɗa da buɗe mashigar ruwa ta Hormuz gaba ɗaya da kuma dakatar da shirin nukiliyar Iran, yayin da rikicin ya ci gaba da haifar da tashin farashin mai da fargabar ƙarin rikici a shiyyar.
