Alƙalin da aka yi garkuwa da shi a Kebbi ya shaƙi iskar ‘yanci

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Rahotanni daga garin Bunza sun bayyana cewa alƙalin babbar kotun da aka yi garkuwa da shi makon da ya gabata Faruku Hassan Bunza ya sami kan sa bayan kwashe sati ɗaya hannun ƴan bindiga da suka yi garkuwa da shi.

Malam Ahmed Bunza ya bayyanawa waƙilin jaridar Blueprint Manhaja da cewa yau Litinin ɗin nan ne labarin dawowar Alƙali Faruku Hassan Bunza ya karaɗe garin na Bunza.
Ya ƙara da cewa kawo yanzu dai babu wani sahihin bayani dangane da ko kuɗi ne aka biya ko kuma da wace manufa ce aka ɗauke shi amma dai ya dawo gida.

Haka-zalika wani ɗan uwan sa ya bayyana cewa iyalan alƙalin ba su fitar da wani bayani ba amma dai nan gaba kaɗan za su yi bayani sai dai sun yaba wa gwamnatin jihar Kebbi da hukumomin tsaro da ƴan uwa da abokan arziki bisa ga addu’o’i da kuma irin rawar da suka taka na ganin alƙalin ya dawo cikin iyalan sa.

A ɗaya ɓangaren kuma babu wani bayani daga rundunar ƴan sandan jihar Kebbi dangane da wannan lamarin saboda jami’in hulɗa da Jama’a na rundunar SP Bashir bai ɗauki waya ba.

By ukarofi

Leave a Reply