Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Dubban mutane ne suka tarbo ɗan takarar kujerar mataimakin gwamnan jihar Kebbi Dokta Musa Muhammed Zagi ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar ADC ta jihar Kebbi Injiniya Sufiyanu Bala a karon farko bayan tabbatar da shi a matsayin ɗan takara.
Dokta Musa Zagi ya bayyana wannan ranar a matsayin rana ta musamman a rayuwar sa saboda irin yadda ƴan uwa da abokan arziki da masoya suka bar harkokin su suka ba shi lokacin su.
Ya ce wannan ba ƙaramin abin alfahari ba ne ganin yadda dubban mutane suka tarbo shi saɓanin yadda a ke yi wa waɗansu ihu da jifa yayin da suka ziyarci mazaɓun su.
Ya bayar da tabbacin insha Allahu za su yi ƙoƙarin kawo canji mai ma’ana idan suka kafa gwamnati. Ya janyo hankalin al’umma kan yankan katin jifar ƙuri’a wacce ita ce babban makamin yaƙin da ya ke tafe na shekarar 2027 musamman a irin wannan lokacin da kowa ke ji a jikin sa tun kama daga rashin tsaro, talauci da yunwa.
Da ya ke jawabi, shugaban Jam’iyyar ADC ta jihar Kebbi Injiniya Sufiyanu Bala ya nuna gaisuwar sa da irin karɓuwar da Dokta Musa Zagi ya samu sanadiyyar irin yawan jama’a da suka tarbo shi suka raka shi zuwa gidan sa.
Ya bayyana cewa jam’iyyar ADC tana samun karɓuwa daga ko ina faɗin ƙasar nan duk da irin bita da ƙulli da a ke yi mata. Ya yi kira ga al’umma da kowa ya fito ranar zaɓe ya jefa ƙuri’ar sa sannan kuma ya tsare ta don ita ce damar sa ta kare mutuncin sa.
