
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mutumin da ya yi iƙirarin shi ne Darakta-Janar na Hukumar Ci-gaban Zuba Jari na Ƙasashen Waje ta Shugaban ƙasa (PFIPC) da ake cece-kuce kan wanzuwarta, Adeniyi Adeyemi ya ture zarge-zargen da ke cewa shi kaɗai ne wanda ya kafa ta, yana mai zargin ma’aikatu da dama, rassa da hukumomin Gwamnatin Tarayya da amincewa tare da yin hulɗa da ita.
Rahotanni sun bayyana cewa, Adeyemi, wanda a yanzu yake hannun hukumar ‘yan sanda, ya yi wannan iƙirari ne ta hannun lauyoyinsa a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Festus Akhigbe, ranar Lahadi.
Ya kuma nemi a ba shi damar zuwa gaban kwamitin bincike na wucin-gadi na Majalisar Wakilai da aka ɗora wa alhakin gudanar da bincike akan al’amarin.
Lauyoyin nasa sun nemi a ba su damar gabatar da Adeyemi a gaban kwamitin, wanda ɗan majalisa, Yusuf Gagdi ke jagoranta, inda suka yi gargaɗin cewa dukkan wani rahoto da za a bayar akansa ba tare da ba shi damar jin ba’asi daga gare shi ba, tauye masa ‘yanci ne da dokar ƙasa ta ba shi a matsayinsa na ɗan Nijeriya.
Haka kuma, sun yi watsi da abin da suka kira da yunƙurin nuna Adeyemi a idon jama’a a matsayin wanda ya ƙagi wata hukumar Gwamnatin Tarayya ba tare da sahalewar kowace hukuma ba wajen samuwa da kafa ta.
A cewar sanarwar, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) ta tabbatar da samun takardun da aka alaƙanta da hukumar da kuma samar mata da gurbin ofishi a Sakatariyar Tarayya.
Kazalika, tawagar ta kirayi mahukunta da su faɗaɗa bincike musamman akan ƙungiyoyin al’umma, masana shari’a, masu sanya ido masu zaman kansu da dukkan hukumomin da aka alaƙanta da al’amarin domin tabbatar da gaskiya da adalci a kai.
