
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Shugaban mulkin Sojin Nijeriya, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya bayyana yadda Gwamnatin Tarayya ta biya ‘yan ƙabilar Igbo diyya akan asarar dukiyoyi da suka fuskanta yayin Yaƙin Basasa na Nijeriya, yana mai bayar da kariya ga tsare-tsaren tattali da suka biyo bayan yaƙin da gwamnatinsa ta aiwatar.
Haka kuma, Gowon ya yi watsi da sukar tsawon lokaci akan Kwamishinan Kuɗi na Tarayya a wancan lokaci, marigayi Cif Obafemi Awolowo na matakin tsarin biyan Fam 20 na bayan yaƙin, yana mai cewa gwamnatin ce da ɗauki matakin samarwa ba Awolowo ba kaɗai.
Tsohon shugaban, wanda ya mulki Nijeriya daga 1966 zuwa 1975, ya ce saɓanin iƙirarin da ake yawan yaɗawa, ‘yan Nijeriya masu kuɗi a bankuna gabanin yaƙin basasar da suka haɗa da ‘yan kasuwa, an biya su kuɗaɗensu har da na ruwa.
Yakubu Gowon ya bayyana haka ne a littafinsa da aka wa laƙabi da “My Life of Duty and Allegiance”, inda ya yi bayanin yadda aka gudanar da harkokin kuɗaɗen Nijeriya bayan yaƙin wanda ya ce an ɗauki matakin ne a ƙarƙashin Majalisar Zartarwar ta Ƙasa (FEC) tare da cewa Awolowo ya yi aiki ne kaɗai a matsayin kwamishinan (minista) a zamanin mulkin nasa.
Yaƙin basasar, wanda aka fara a 1967 kuma aka kammala a 1970, ya yi silar gwamnati ta samar da tsarin “no victor, no vanquished”, ma’ana yaƙin da aka kammala babu tabbataccen wanda ya yi nasara ko ya faɗi, inda shugaban ya ƙaddamar da shirye-shiryen sulhu, sake ginawa da gyara a sassan Jihar Gabas ta Tsakiya.
Da yake tsokaci da matakin gwamnatin nasa, Gowon ya bayyana cewa sun samar da sauyin kuɗin da ake amfani da shi a lokacin bayan gagarumar sata da aka yi a rassan Babban Bankin Nijeriya na Benin da Enugu, yana mai cewa da dama daga cikin abin da mutane suka mallaka ya zama ba halastaccen kuɗi ba a Nijeriya.
Ya kuma ce, hatta kuɗin yankin Biafara ba shi da darajar da za a iya canzawa a ko’ina a duniya, yana mai cewa saboda yawansa ne ya sa gwamnatin ta ƙi karɓa da nufin canzawa don kada ƙasar ta shiga halin matsin tattalin arziƙi.
A cewarsa, “ƙwararru kan harkar tattali sun shawarci Gwamnatin Tarayya ta rage biyan zuwa ba wa kowane baligin Biafara Fam ɗin Nijeriya 20 ba tare da la’akari da adadin kuɗin Biafara da ya dawo da su ba.
Kazalika, ya ce gwamnatin ta kuma kafa ƙarin wasu matakai na tabbatar da farfaɗo da lamuran yankunan da yaƙin ya shafa.
