Ambaliya ta rutsa da ƙananan hukumomin Yobe huɗu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Asabar wani mamakon ruwan da aka zabga a sassan ƙananan hukumomin Damaturu, Nguru, Machina da Bursari na Jihar Yobe ya haddasa ambaliya, lamarin da ya yi sanadiyyar damejin wasu gidaje da kai agajin gaggawa daga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA).

SEMA ta sanar da batun a wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi, 2 ga Agusta, 2026.

Blueprint Manhaja ta gano cewa hukumar ta samu kiran buƙatar agajin gaggawa daga jagororin al’umma hukumomin tsaro da hukumomin ƙananan hukumomi bayan ruwan saman da ya haɗe ƙauyuka da dama.

Yankunan da ambaliyar ta fi shafa a Damaturu sun haɗa da Moduri, Abbari Sabon Kwalta, Malari Sabon Kwalta, Pompomari, Sumsumma da kuma Nayinawa.

A Nguru, an samu ambaliya a yankunan New Side Best Centre, Balanguwa Road da wasu ƙauyuka da ke gundumomi tara. Gundumomin Turbangini da Dinani/Lawanti ne iftila’in ya shafa a Ƙaramar Hukumar Bursari, yayin da layin Alhaji Madi, Hausari da garin Machina suka gamu da ambaliyar a Ƙaramar Hukumar Machina.

Hukumar ta kuma ce jami’anta suna aiki tuƙuru wajen gano ainihin girman matakin ɓarnar da ambaliyar ta yi wa gidaje da yankunan da kuma mutanen da ta shafa.

Haka kuma, tawagar haɗakar hukumomin gwamnati na bayar agajin gaggawa na duba matakin ɓarnar da kira ga buƙatar bayar da tallafin jin-ƙai.

By Babaji

Leave a Reply