Reno Omokri da wasu uku na tsaka mai wuya yayin da jakadun Tinubu 65 suka kama aiki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mutane huɗu da Shugaba Bola Tinubu ya amince da su a matsayin jakadu na fuskantar ƙalubale yayin da guda 65 suka samu tantancewar fara aiki a ƙasashen da aka tura su.

A sanarwar da kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa ya fitar, an ce ƙasashe masu karɓar baki sun riga sun amince da jakadu 65, wanda ya kai kusan kaso 97 cikin 100 na dukkan waɗanda aka naɗa.

Sanarwar ta bayyana cewa, tsohon kakakin shugaban ƙasa, Reno Omokri, wanda aka naɗa a matsayin jakadan Nijeriya a ƙasar Mexico, na daga cikin waɗanda har yanzu ba su samu amincewar ƙasar da za su yi aiki ba.

Haka kuma, Olumilua Oluwayimika Ayotunwa, wanda aka naɗa zuwa Japan, na ci gaba da jiran amincewar gwamnatin ƙasar.

Haka ma Grace Bent, ta ƙi karɓar muƙaminta na jakadiya zuwa Togo, yayin da Mohammed Mahmud Lele, wanda aka naɗa jakadan Nijeriya a Aljeriya, ya rasu kafin ya kama aiki, lamarin da ya sa aka samu giɓi a gurbin da ya bari

Ma’aikatar ta ce tana cigaba da tattaunawa da ƙasashen da abin ya shafa domin kammala sauran matakan difulomasiyya, tare da nuna ƙwarin-gwiwar cewa za a samu amincewar da ta rage nan ba da jimawa ba.

A kwanakin baya ne Shugaba Tinubu ya amince da naɗa jakadu 69 ga wasu ƙasashe domin ƙarfafa harkokin difulomasiyyar Nijeriya da ƙasashen waje bayan ofisoshin jakadanci da dama na aiki na tsawon lokaci ba tare da jagorori ba.

By Babaji

Leave a Reply