Kano: Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Bichi ya tallafa wa ‘yan yankin da kuɗaɗe

Spread the love

Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Abubakar Sulaiman Babangida Ɗan Zabuwa ya gudanar da taron ba da tallafin dubu goma-goma na ƙashin-kansa ga mata da maza 300 a Sakatariyar ƙaramar hukumar.

A sanarwar da Jami’ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa manema labarai ta ce, Alhaji Aminu Mammam da ya yi magana a madadin Shugabancin jam’iyya mai mulki a wajen taron, ya ce, wannan ba shi ne karon farko ba, Alhaji Abubakar Sulaiman Ɗanzabuwa ya bayar da irin wannan tallafin kusan sau huɗu zuwa biyar a yankin, inda ya ja hankalin sauran masu riƙe da irin waɗannan muƙamai, su yi koyi da irin ƙoƙarinsa.

“Ba shi kaɗai ba ne yake da muƙami na ƙasa-ƙasa, amma yana daga cikin masu zuciya da ƙoƙari da yake tallafa wa wannan tafiya tamu a Ƙaramar Hukumar Bichi, saboda haka na san yana da burin ci gaba da tallafa wa jam’iyyarmu ta APC. Babu abin da za mu ce da shi sai godiya da addu’a.” Alhaji Aminu Mammam.

A nasa jawabin Mataimakin Shugaban yankin, Alhaji Abubakar Ɗanzabuwa, ya bayyana irin yadda jagororin ƙaramar hukumar ke shimfaɗa ayyukan raya ƙasa da gina al’umma ƙarƙashin jagorancin jam’iyya mai mulki a yankin, musamman Ɗanmajalisar Tarayya, Abubakar Kabir Abubakar da ya zama shakundum a ƙaramar hukumar.

“Yanzu haka, yau za a buɗe wasu cibiyoyi 4 na wutar lantarki waɗanda za su tashi daga nan garin Bichi zuwa Ɗanzabuwa da Ghari da Tsanyawa da kuma wani ɓangare da aka ware wanda iya gidan ruwa na Watari kaɗai zai riƙa bai wa wuta daga yau.

Sannan akwai wani ɓangaren wanda duk Ɗanmajalisa Abba ne zai buɗe da zai riƙa bai wa Kasuwar Dawanau wutar lantarkin daga nan Bichi gaba ɗaya. Kazlika da wata babbar hanya da ita ma zai buɗe wadda za ta shigo garin Bichi daga wajen.” Alhaji Abubakar Sulaiman Babangida.

Sakataren Mulki na yankin, Alhaji Anas Muhammad da ya wakilci Shugaban ƙaramar hukumar, ya bayyana jin daɗinsa tare da fatan ƙarfafa gwiwa na cigaba da assasa tarukan alheri, domin bin sahun manyan jagororin yankin daga kowane ɓangare na mataimakansa.

A ɓangaren waɗanda suka amfana mata da maza, sun yi matuƙar godiya da fatan alheri ga mataimakin Shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar Bichin bisa wannan gagarumin ƙoƙarin da ya saba.

“1- Godiya muke Allah ya saka da alheri ya sa ya fi haka. 2- Wannan tallafi da aka ba mu, Allah ya saka da alheri ya sa mu amfana. 3- Waɗanda suka samu albarkacin amfanar wannan tallafi su taimaka su ce da jama’a kowa ya fito ya yi zaɓe!” In ji waɗanda suka amfana da tallafin.

Taron ya samu halarcin, Tsohon Kantoman Riƙo na Bichi, Alhaji Ahmad Kado, Sakataren Jam’iyyar APC, Alhaji Aminu Muhammad, Mataimakiyar Shugabar Matan Jam’iyyar APC, zaɓaɓɓun kansiloli da naɗaɗɗu, masu ba da shawara da kuma Malam Usman Magaji a madadin al’ummar Ɗan Zabuwa.

By Babaji

Leave a Reply