
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaro na Sashe na 2 na Atisayen FANSAR YAMMA da kaa tura sansanin Forward Operating Base (FOB) a Kasuwan Daji da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda a Jihar Zamfara, sun yi nasarar daƙile wani yunƙurin harin ‘yan ta’adda.
Rundunar Sojin ta ce, harin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 1:40 na safiyar Lahadi, ya yi sanadiyyar raunata mayaƙan ‘yan ta’adda da dama, lamarin da ya tilasta musu ja da baya sa kuma ceto wasu fararen hula guda tara bayan wani atisaye da ua biyo baya.
A cewar rundunar, wani jami’in soji guda da ɗan sanda sun rasu a yayin ba-takashi da maharan, a lokacin da suke ƙoƙarin afkawa cikin sansanin sojojin.
Rundunar ta ce baya ga mutuwar soja da ɗan sandan, wasu sojoji biyu sun samu raunukan harbin bindiga, kuma an kai su asibiti domin samun kulawa.
Haka kuma, musanta rahotannin da ke cewa jami’an tsaro shida ne suka mutu, tana mai cewa mutum biyu ne kaɗai suka rasa rayukansu.
Kazalika, rundunar ta ce dakarunta sun cigaba da gudanar da samame a yankin domin tantance irin asarar da maharan suka yi tare da tabbatar da tsaron al’ummar yankin.
Har ila yau, ta jaddada aniyarta ta cigaba da ƙaddamar da hare-hare akan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda domin dawo da zaman lafiya a Arewa maso Yamma da ma ƙasa baki ɗaya.
