Ƴan sanda sun cafke telan da ke ɗinka tutar Rasha a Kano

Spread the love

Ƴan sanda sun yi nasarar cafke wani tela mai suna Ahmed wanda ake tuhuma da ɗinka tutar ƙasar Rasha ya na rabawa mutane a yayin zanga-zanga.

Kakakin rundunar ƴan sandan Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da hakan ta wani saƙon WhatsApp.

Ya bayyana cewa an kama Ahmed ta tutar Rasha guda bakwai,wanda yake kira da cin amanar ƙasa da yi mata zagon ƙasa.

Wannan na zuwa ne bayan jawabin da shugaban ƙasa yayi bai gamsar da mutane ba, sai a ka ga mutane sun fito su na ɗaga tutar ƙasar Rasha.

By ukarofi