03
Aug
Daga DAUDA USMAN a Legas Wani babban mai faɗa a ji a kasuwar gwarin Illeoko ta Ƙaramar Hukumar Alimosho dake cikin birnin Ikko, Alhaji Mu'awuya Idris Simoli ya bayyana cewar shi da sauran shuwagabannin kasuwar ta gwarin Illeoko suna fuskantar manyan ƙalubale mai yawa a kasuwar da kewayenta gaba ɗaya. Alhaji Mu'awuya Idris Simoli ya furta hakan ne a Legas a lokacin da yake zantawa da jaridar Blueprint Manhaja dangane da al'amuran da suka shafi harkokin kasuwancin gwari a Legas baki ɗaya. Simoli ya ci gaba da labarta wa Jaridar Blueprint Manhaja cewar haƙiƙa tun daga wancan lokacin ya zuwa…
