Gwamnatin Kaduna za ta tallafi manoman citta a jihar

Spread the love

Daga AMINA YUSUF ALI

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin Kaduna tare da hukamar gwamnatin Tarayya za su tallafa wa manoman citta da suka tafka hasara a kakar bara

Gwamnatin Kaduna tare da hukamar gwamnatin Tarayya za su tallafa wa manoman citta da suka tafka hasara a kakar bara
Biyo bayan ibtila’in da ya afka wa manoman Citta da ya yi sanadiyyar tafka gagarumar asara a kakar noman bara da wasu manoman suka rasa ilahirin amfanin gonarsu, jin ƙai da tallafi na tafe cikin gaggawa daga mahukunta daga Kaduna da gwamnatin Tarayya.

Asusun tallafa wa manoma na gwamnatin tarayya NADF da hukumar inganta aiyukkan noma ta jihar Kaduna KADA sun haɗa ƙarfi da karfe domin tallafa wa manoman citta dake ƙananan hukumomi bakwai a jihar Kaduna.

Gwamnati ta yanke wannan shawara ne sanadiyyar varkewar cutar ‘Blight’ da manoman citta a jihohin Kaduna, Nasarawa da Filato da Babban Birnin Tarayya Abuja suka yi fama da ita a bara.

A dalilin haka manoma da dama a waɗannan jihohi ba za su samu daman yin noman citta a bana ba.

A jihar Kaduna NADF da KADA a ƙarƙashin shirin tallafa wa wa manoma na GRATE kowanne namomin citta zai samu buhunan taki NPK 4, Urea biyu, buhun masara ɗaya, irin dawa da magungunan feshi.

Wakilin NADF Samuel Aende ya sanar da haka a zaman da suka yi da manoma da masu ruwa da tsaki a fannin noma a ƙaramar hukumar Kachia ranar Talatar da ta gabata.

Aende ya ce daga nan za su ziyarci ƙananan hukumomin Kachia, Jaba, Kagarko, Zangon Kataf, Kaura, Jema’a da Sanga domin ganawa da manoma da masu ruwa da tsaki a yankin.

Wakilin KADA David Jonathan ya ce wannan shiri da gwamnati ta yi zai taimaka wajen inganta noman citta da rayuwar manoma a jihar.

Shugaban ƙaramar hukumar Kachia Victoria Saidu ta Mika godiyarta ga gwamnati sannan ta hori manoma da su tabbata sun yi amfani da tallafin da za su samu ta hanyoyin da ya kamata.

Shugaban ƙungiyar manoman citta na kasa reshen jihar Kaduna Nuhu Dauda a madadin manoman jihar ya miqa godiyarsa ga Shugaban ƙasa Bola Tinubu da gwamnan jihar Kaduna Uba Sani bisa wannan tallafi da suka samu domin agaza musu da kuma rage raɗaɗin rashin da suka yi a bara.

By Editor