Daga AMINA YUSUF ALI
Rahotanni dai sun bayyana cewa, ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar na shirin janye matakinsu na ficewa daga ƙungiyar Ecowas mai raya tattalin arzikin qƙasashen Afirka ta Yamma.
Sanata Ali Ndume – wanda ɗan majalisar ƙungiyar Ecowas ɗin ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Kano, a yayin da majalisar ƙungiyar ke ci gaba da gudanar da taronta a jihar.
Dan majalisar ya ce an cimma duk wani abu da ake buƙata domin maido da ƙasashen cikin ƙungiyar ta Ecowas.
“An riga an warware saɓanin da ya kai ga ɗaukar matakin fita daga ƙungiyar, kuma a yanzu duka ƙasashen sun huce daga fushin da suke yi da Ecowas, saboda haka ga dukkan alamu a shirye suka su dawo cikin ƙungiyar”, in ji ɗan majalisar.
Ƙasashen uku sun ɗauki matakin fita daga ƙungiyar ne bayan da Ecowas ta yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji sukayi a ƙasashen, tare da sanya musu jerin takunkumai.
