Mafi ƙarancin albashi: NLC ta ƙara matsa lamba a kan gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga AMINA YUSUF ALI

Ƙungiyoyin ‘yan ƙwadago ta NLC da TUC sun nemi gwamnatin Bola Ahmad Tinubu da ta biya Naira 497,000 maimakon Naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

A taqaice dai ma wato sun sassauta abin da suke buƙata gwamnati ta biya a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar zuwa naira 497,000.

A baya dai ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce dage a kan Naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi da suke son gwamnatin ƙasar ta amince da shi.

Yayin cigaba da tattaunawar a ranar Talatar da ta gabata, ƙungiyoyin sun kuma yi watsi da sabon ƙudirin da gwamnati ta gabatar na naira 54,000 a matsayin albashi mafi ƙaranci.

Haka kuma a ranar Laraba kwamitin ƙarin albashin ya bai wa NLC tayin naira 57,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin, inda nan take ƙungiyar ƙwadagon ta yi fatali da tayin. Har dai yanzu ba a cimma matsaya ba tsakaninsu.

By Editor