Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ƙasashe 58 daga cikin 164 mambobin Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO) sun nuna goyon bayansu ga buƙatar neman shugabar ƙungiyar Ngozi Okonjo-Iweala ta yi tazarce wa’adi na biyu.
Ƙasashen sun bayyana goyon bayansu ne ga Okonjo-Iweala a babban taron ƙungiyar da aka gudanar ranar Litinin, kamar yadda WTO ta wallafa a shafinta na intanet.
“Ƙungiyar Afirka da ake kira Africa Group ne ta gabatar da buƙatar cewa shugabar a shirye take ta yi wa’adi na biyu, kuma ta gabatar da buƙatar cewa a fara bin matakai na sake zaɓar ta ba tare da ɓata lokaci ba,” a cewar sanarwar.
Mambobin ƙungiyar 58 sun bayyana goyon bayansu ga Okonjo-Iweala a babban taron na WTO tare da yin kira ta fito ta bayyana aniyarta ta neman wa’adi na biyu.
Ƙasashen sun jinjina wa shugabar kan nasarorinta da kuma jajircewarta a wa’adinta na farko.
Okonjo-Iweala ta ce ta saurari buƙatar ƙasashen kuma za ta yi nazari game da buƙatar.
Okonjo-Iweala ‘yar Nijeriya, ita ce ta bakwai a matsayin shugabar WTO. Ta karɓi rantsuwar kama aiki ne a ranar 1 ga Maris a wa’adin farko na shekara huɗu kuma wa’adin zai ƙare ne a ranar 31 ga Agustan 2025.
Tsohuwar ministar kuɗi ta Najeriya ta kasance mace ta farko kuma ‘yar Afirka da ta taɓa rike muƙamin shugabar ƙungiyar Cinikayya ta Duniya.
