Zanga-zanga: Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci ta gargaɗi matasa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci ta Nijeriya ta yi kira ga matasa da su nisanci zanga-zanga da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar.

Shehu Muhammad Maƙarfi, wanda ya wakilci majalisar, a wajen taron bita na kwanaki biyu da Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta shirya a Gombe, mai taken “Dogaro da Kai da Kame Kai: Mafi Girman Dabara ga Malamai a cikin Da’awa,” ne ya sanar da haka.

Maƙarfi ya bayyana cewa duk wanda ke ƙarfafa wa matasan Nijeriya su yi zanga-zanga, ba ya yin aiki da maslaha ga ƙasa.

“Zanga-zanga koma-baya ce ga Nijeriya, musamman a Arewacin inda muke jin daɗin zaman lafiya.

“Ba za mu bari bata-gari su tarwatsa zaman lafiyarmu ba,” ya jaddada.

Ya yi kira ga Gwamnan Jihar Gombe, a matsayin Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, da ya ɗauki matakai don haɗa malamai da sarakuna wajen ƙarfafa zaman lafiya da yi wa jama’a gargaɗi kan haɗarin zanga-zanga.

Maƙarfi ya yi gargaɗin cewa wasu matasa na iya amfani da damar wajen aikata abubuwan ɓarna.

Ya ba da misalai na abubuwan da suka faru a baya inda matasa suka ƙwace kadarori da wayoyin hannu.

A madadin Majalisar Ƙolin Shari’a, Maƙarfi ya yi kira ga gwamnati da ta hana zanga-zangar tare da samar da hanyoyin samun abin dogaro don rage wahalar da jama’a ke fama.

Ya kuma ba da shawarar kafa ofishin hadin gwiwa na harkokin addini don sauƙaƙa sadarwa tsakanin gwamnati da Majalisar Ƙolin Shari’a ta Ƙasa.

A cewarsa, hakan zai ba da damar rijistar makarantu da masallatai, da kuma tsarin daidaiton harkokin addini.

Sheik Sani Yahaya Jingir, shugaban Jama’atu Izalatu Bidi’ah Wa Iƙamatis Sunnah (JIBWIS), wanda Sheikh Hamza Adamu ya wakilta, ya bayyana cewa ba za su goyi bayan zanga-zangar ba, yana ba da misalai na ƙasashe kamar Libiya da Sudan, inda zanga-zanga ta haifar da rashin tsaro da rikici.

By ukarofi