Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa (CNG), Kwamared Jamilu Aliyu Chiranci, ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da Shugaba Tinubu da su tashi tsaye su yi duk mai yiwuwa domin hana abin da ke shirin faruwa a ƙasar.
Kwamared Aliyu ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ƙungiyar ta kira a cikin makon nan, sa’ilin da ake tsaka da batun gudanar da wata zanga-zanga a faɗin ƙasar a kan tsadar rayuwa da harkar tsaro da ake fama da su musamman a Arewacin ƙasar.
Shugaban ƙungiyar ya ce sanin kowa ne al’umma suna cikin mawuyacin hali da rugujewar tattalin arziki da yawaitar ta’addanci da ya ɗaiɗaita harkar noma da kiwo da tsadar kayan masarufi.
“Mun kira taron manema labarai ne domin mu nusar da maigirma Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu akan zangar-zangar da ake shiryawa a ƙasar, mu nuna masa ga halin da ƙasar nan ke ciki, ko da yakan kasance waɗanda ya kamata su ba shi labarin ba sa faɗa mishi gaskiyar al’amari.
“Don mutumin da zai ba shi wani labari [Tinubu] wanda ya sha bamban da cewa al’ummar Nijeriya suna wahala, komai na tafiya daidai, to labari ne na ƙanzon kurege.
“Wannan ne ya sa muka fito domin mu sanar da shi domin ya kawo abubuwan da za su canja wannan al’amarin,” inji shi.
Kwamared Aliyu ya ƙara da cewa ya kamata Shugaba Tinubu ya fitar da al’umma a cikin halin ƙangin da suke ciki duba da janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi da sauran matsalolin da suka shaƙe wa ƙasar maƙogoro.
Kwamared Jamilu Aliyu Chiranci ya ƙara cewa talakawa sun gaji da gafara sa alhalin har yanzu ba su ga ƙaho ba, inda ya ce sau tari gwamnati tana iƙirarin sun san halin da ake ciki ‘a ƙara haƙiri’ amma sun kasa yin haƙuri da wasu buƙatu na ƙashin kansu, inda ya ce ya kamata Shugaba Tinubu da Mataimakinsa su dakatar da sayen jirage da motoci da gina gidan Mataimakin Shugaban Ƙasa da a cewarsa an kashe maƙudan kuɗaɗe?
“Har yanzu ba mu ji inda aka ce an zaftare kudin wata hidima ta Shugaban Ƙasa ko Mataimakinsa ba saboda babu kuɗi. Saboda haka ta yaya talakawa za su yarda cewa a yi haƙuri za a yi wani abu, kullum sai gafara sa amma har yanzu ba mu ga ƙaho ba.”
Daga ƙarshe Shugaban ƙungiyar ya ce ba sa fatan a shiga zanga-zanga, domin a a cewarsa ba sa ƙaunar a hargitsa ƙasar ta ƙi zama lafiya. Ya ce Shugaba Tinubu ya fito ya yi abin da ya kamata musamman tallafin man fetur.
Idan ba a manta ba a cikin makon jiya ne Ministan Yaɗa Labarai, Muhammed Idris ya ce Gwamnatin Tarayya ta raba wa kowa ce jiha tirela 20 na shinkafa domin raba wa talakawa don rage raɗaɗin halin da ake ciki.
Sai dai masu sharhi na ganin cewa wannan kaɗai ba shi ne mafita ba.
