Gwamnati ta dakatar da jirgin Air Nigeria har sai baba-ta-gani

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar cewa, ta dakatar da aikin kamfanin jirgin saman Nijeriya, wato Air Nigeria.

Sanarwar wadda aka fitar a ranar Litinin ta ce, dakatarwar ta har baba-ta-gani ce.

Ministan Sufurin Jirgin Sama, Festus Keyamo, shi ne ya bayyana haka yayin da yake ba da bayani kan ayyukan ma’aikatarsa a matsayin ɓangare na cika Shuga Bola Tinubu shekara guda a ofis.

Da yake ƙarin haske kan dalilin dakatarwar, Keyamo ya ce, jirgin da aka nuna cewa ta Nijeriya ne ba gaskiya, rufa-rufa ce kawai aka yi wa lyan ƙasa a wancan lokaci.

By Editor