Kasuwanci

Ƙarin kuɗin wuta: NLC ta jijjiga kamfanonin JEDC, YEDC

Ƙarin kuɗin wuta: NLC ta jijjiga kamfanonin JEDC, YEDC

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), ta rufe babban ofishin kamfanin rarraba wutar lantarki na Jos Electricity Distribution Company (JEDC) a Jihar Filato kan ƙarin kuɗin wuta. Binciken Manhaja ya gano NLC ta rufe babbar ƙofar shiga kamfanin lamarin da ya haifar wa ma'aikatan DisCo tsaiko wajen shiga ofishin. Kazalika, NLC ta girgiza kamfani rarraba wutar lantarki na Yola Electricity Distribution Company (YEDC) a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba duk dai kan batun ƙarin kuɗin wuta. Dukkan wannan ya faru ne a ranar Litinin a ci gaba da gwagwarmayar da NLC ke yi wajen tabbatar da 'yan ƙasa…
Read More
Tinubu ya umarci CBN ya dakatar da aiwatar da harajin tsaron intanet

Tinubu ya umarci CBN ya dakatar da aiwatar da harajin tsaron intanet

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ya dakatar da aiwatar da harajin rabin kashi ɗaya (0.5%) na tsaron internet wanda ya tada ƙura a ƙasa, tare da neman a sake nazarin dokar. Idan ba a manta ba a ranar 6 ga Mayu, CBN ya fitar da sanarwa tare da umuryar bankuna da su ɗabbaƙa sabon haraji na tsaron intanet. Sabuwar dokar ta nuna za a riƙa biyan kashi 0.5 na hada-hadar kuɗaɗe ta intanet sannan a tattara a zuba a asusun Taaron Intanet ƙarƙashin kulawar Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara…
Read More
CBN ya bai wa masu POS watanni biyu su yi rajista da CAC

CBN ya bai wa masu POS watanni biyu su yi rajista da CAC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umurci duk masu sana’ar POS a ƙasar nan da su yi rajistar kasuwancinsu da hukumar kula da harkokin kamfanoni (CAC) nan da watanni biyu. An bayyana hakan ne bayan wata ganawa tsakanin Fintechs da Shugaban CAC na Ƙasa, Hussaini Magaji (SAN) a Abuja a ranar Litinin. Shugaban na CAC ya ce wa’adin watanni biyu na yin rajistar wanda zai ƙare a ranar 7 ga watan Yuli, ba an yi ba ne don muzgunawa wata ƙungiya ko ɗaiɗaikun mutane ba, amma “ya yi daidai da ƙa’idojin doka da kuma umarnin…
Read More
Za mu yi gagarumar zanga-zanga idan ba a soke harajin tsaron intanet ba – TUC

Za mu yi gagarumar zanga-zanga idan ba a soke harajin tsaron intanet ba – TUC

Daga SANIAHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC a Nijeriya ta yi barazanar gudanar da gagarumar zanga-zanga tare da dakatar da al'umura a faɗin ƙasar matuƙar gwamnatin tarayya ba ta soke sabon harajin tsaron intanet da Babban Bankin ƙasar ya ɓullo da shi ba. Ƙungiyar ta yi barazanar ce a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, wadda ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar, Festus Osifo. Hakan na zuwa ne bayan ita ma ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta soki lamirin sabon harajin, wanda ta bayyana a matsayin wani gagarumin nauyi da gwamnati ke ɗora wa talaka. A ranar Talata…
Read More
AEDC, Kaduna DisCo sun zabtare farashin wutar lantarki

AEDC, Kaduna DisCo sun zabtare farashin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH Kamfanin raba lantarki na Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ya ba da sanarwar rage farashin wutar lantarkin da yake raba wa kostomominsa na runukunin Band A daga N225/kWh zuwa N206.80/kWh. A ranar Litinin AEDC ya bayyana haka saƙon dabya wallafa a shafinsa na X. Sanarwar ta ce, “Muna farin cikin danar da rage farashin wuta ga kostomominmu na Band A, an yi ragin ne daga N225/kWh zuwa N206.80/kWh wanda ya fara aiki daga yau, 6 ga Mayu, 2024." Kamfanin ya kuma bai wa abokan mu'amalarsa na Band A ɗin tabbacin samun wutar lantarki na sa'o'i 20 zuwa…
Read More
IKEDC ya rage farashin wutar lantarki

IKEDC ya rage farashin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH Kamfanin Ikeja Electricity Distribution Company ya rage wa kostomominsa na rukunin Band A kuɗin wuta da za su biya zuwa N206.80 kan kowane kilowat a sa'a guda maimakon N225 da hukumar kula da lantarki, NERC a taƙaice ta amince da shi. Mai magana da yawun IKEDC, Olufadeke Omo-Omorodion, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin. Sanarwar ta ƙara da cewa, ragin kuɗin wutar zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 6 ga Mayu, 2024. Haka nan, ta ce a maimakon N225/Kwh da kostomominsu na Band A su biya bisa la'akari da…
Read More
Kotu ta haramta wa NERC aiwatar da ƙarin kuɗin wutar lantarkin

Kotu ta haramta wa NERC aiwatar da ƙarin kuɗin wutar lantarkin

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Kano ta ba bai wa Hukumar Kula da Wutar (NERC) da kamfani Kano Electricity Distribution Company (KEDCO) kan kada su aiwatar da ƙarin kuɗin wutar lantarkin da aka yi ga masu amfani da wutar lantarki na Band A. Kwanankin bayana ne NERC ta umarci kamfanonin rarraba wutar lantarki da su ƙara kuɗin wutar da suke bai wa kostomominsu na rukunin Band A domin samun wadatar wutar lantarki. Sai da daman 'yan Nijeriya sun soki matakin na NERC musamman yadda hukumar ta ɗora da yawan kostomomin nata a tsarin Band A duk…
Read More
Kamfanonin waya sun nemi Tinubu ya ba su haɗin kai don tsauwala farashi

Kamfanonin waya sun nemi Tinubu ya ba su haɗin kai don tsauwala farashi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamfanonin manyan layikan sadarwar da su ke aiki a Nijeriya, wato Glo, MTN, Airtel da 9Mobile, sun roƙi Gwamnatin Tarayya a karƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta sassauta wasu ƙa'idojin da ta saka wa kamfanonin, don ba su damar ƙara tsauwala farashin kuɗin kiran waya da na data. A cewar kamfanonin, tsarin kula da farashin na yanzu bai dace da yanayin matsin tattalin arziki ba, don haka suke neman taimakon gwamnati, don magance ƙalubalen farashin. Kamfanonin sadarwa guda huɗu sun ce, su kaɗai ne ba su yi ƙari kan farashinsu ba, wanda hakan ke…
Read More
Yadda babban kantin ƙasar Sin da ke Abuja ya hana ‘yan Nijeriya shiga

Yadda babban kantin ƙasar Sin da ke Abuja ya hana ‘yan Nijeriya shiga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani babban kanti na kasar China da ke Abuja ya fuskanci suka bayan da aka ce ya hana kwastomomin Nijeriya shiga shagon. Babban kantin da ke Babbar Cibiyar Kasuwanci na ƙasar Sin, dake kan titin Umaru Musa Yar’adua a Abuja, an yaba shi a matsayin wurin da ake amfani da abinci da abin sha na ƙasar Sin. A cikin faifan bidiyo, ana iya ganin mutumin ɗan Nijeriya da ba a san ko wanene ba yana nuna ɓacin rai da kaɗuwa yayin da aka kore shi a ƙofar babban kantin. Rahotanni sun ce hukumar ta…
Read More
Gwamnatin Nijeriya ta ɗora alhakin katsewar lantarki a kan kamfanonin wuta da masu zagon ƙasa

Gwamnatin Nijeriya ta ɗora alhakin katsewar lantarki a kan kamfanonin wuta da masu zagon ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a AbujaMinistan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi tir da ayyukan ‘yan zagon ƙasa a harkar wutar lantarki, inda ya ɗora alhakin katsewar wutar lantarki a ƙasar nan a kansu. Mista Adelabu ya bayyana hakan ne yayin wani shiri mai taken “Confronting Nigeria’s Power Challenge as the Nation Migrates to Multi-Tier Electricity Market” a ranar Talata a Abuja. Kwamitin samar da wutar lantarki na majalisar wakilai ne ya shirya shirin. Ministan ya ce ‘yan zagon ƙasa da ‘yan daba suna aikata muggan laifuka ne don son kai domin daƙile yunƙurin tabbatar da samar da wutar lantarki…
Read More