28
Apr
Daga SANI AHMAD GIWA a AbujaMinistan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi tir da ayyukan ‘yan zagon ƙasa a harkar wutar lantarki, inda ya ɗora alhakin katsewar wutar lantarki a ƙasar nan a kansu. Mista Adelabu ya bayyana hakan ne yayin wani shiri mai taken “Confronting Nigeria’s Power Challenge as the Nation Migrates to Multi-Tier Electricity Market” a ranar Talata a Abuja. Kwamitin samar da wutar lantarki na majalisar wakilai ne ya shirya shirin. Ministan ya ce ‘yan zagon ƙasa da ‘yan daba suna aikata muggan laifuka ne don son kai domin daƙile yunƙurin tabbatar da samar da wutar lantarki…
