30
Mar
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Kare Haƙƙin Mallaka ta Nijeriya, NCC, ta gurfanar da Kamfanin Sadarwar MTN da wasu mutane huɗu a gaban kotu bisa zarginsu da keta haƙƙin mallaka. An shigar da aarar mai lamba FHC/ABJ/CR/111/2024 a babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Litinin. Sauran mutane huɗu da ake tuhuma a shari’ar su ne; Karl Toriola, shugaban MTN na Nijeriya, Nkeakam Abhulimen da Yahaya Maibe. A cikin tuhume-tuhume uku, NCC ta yi zargin cewa waɗanda ake tuhumar, a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2017, “sun amfani da fasahar da ba tasu ba”, sun keta ayyukan waƙa na wani mawaƙi,…
