Nijeriya ta zama ƙasa ta 4 a jerin ƙasashe 10 mafiya amsar bashi a Bankin Duniya

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai ƙasar Nijeriya ta taka matsayi na 4 na ƙasashen da suka fi kowa cin bashi a jerin sunayen ƙasashe na IDA na Bankin Duniya (ƙasashe masu yin rance a bankin). A yanzu haka ana bin ƙasar bashin Dalar Amurka biliyan 14.3.

Nijeriya ta daɗe a wannan matsayi nata na huɗu a jerin ƙasashe da ke ƙungiyar (IDA) masu rancen. Tun bayan da ta baro matsayi na 5 a Yunin shekarar 2022.

Duk da Nijeriya ta kasance mai matsayi na 4, ta tara wa kanta bashin Dalar Amurka biliyan 1.3 a cikin shekara guda kacal.

Wannan jawabi yana ƙunshe ne a rahoton binciken kuɗi na Bankin Duniya na shekara-shekara na shekarar 2022 . Rahoton ya nuna yadda Nijeriya ta tsallaka zuwa matsayi na 4 a jerin da ƙarin bashin da ta karva na Dalar Amurka biliyan 13 ranar 30 ga Yunin, 2022.

Rahoton Bankin Duniya ya ƙara da cewa, duk da ƙarin bashin da Nijeriya ta sake ciyowa a shekarar 2023, abinda ya sa jimillar kuɗin da ake binta ya kai Dalar Amurka biliyan 14.3, har yanzu dai ba ta motsa daga matsayinta na huzu ba.

Ƙasar Bangladesh, ita ce a saman kowacce ƙasa a jerin bashin. Domin abinda ake binta ya kai Dalar Amurka biliyan 19.3. Ta doke ƙasar Indiya wacce da ita ce jagaba a cikin jerin bashin. A halin yanzu bashin na Indiya ya miqa zuwa Dalar Amurka biliyan 17.9, abinda ya sa ta zama a matsayi na biyu.

Ƙasar Pakistan ita ma har yanzu ba ta motsa daga matsayinta na uku ba a matsayin ƙasa ta uku da ta fi cin bashi. Ita ma bashinta ya tasamma Dalar Amurka biliyan 6.9.

Bisa la’akari da rahoton binciken kuɗi na shekarar 2022 na Bankin Duniya, Nijeriya ita ce ta fi kowacce qasa a Afirka cin bashin Babban bankin, sai kuma wasu daga jiga-jigan karɓar bashin na Bangladesh, Indiyaa, da Pakistan, dukkansu daga Asiya suke.

Hakazalika, a rahoton shekara-shekara na 2023, Nijeriya ta kasance daga cikin jiga-jigan ƙasashe 10 da suke sake karɓar sabon bashi a banan.