Falasɗinu: Jinin mata da yara na kwarara!

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A gaskiya a ƙa’idar tsarin yaƙi bai dace a tava rayuwar mata da yara da ma tsoffi ba. Hakanan duk wanda ba hari ya kawo ko ya na riƙe da makami da a ke gwabzawa da shi ba, to ƙyale shi a ke yi a yanayin yaƙi. Duniya ko ba ta adalci; amma akwai dokokin da ta ke bi ko ta ke kan su. In da Majalisar Ɗinkin Duniya na iya tsawatawa a ji, to haƙiƙa da wasu rayukan da ba su da hannu a faɗa ba su tavu ba.

Ya kamata a duba yadda kowane ɓangare a faɗan Isra’ila da Falasɗinawa ke gudanar da lamuran sa don kaucewa wuce gona da iri ko jefa laifi na son zuciya. A fili dai an san Isra’ila na da makaman da kowace qasa ta duniya za ta iya alfahari da su don inganci da sanin dabarun yaƙi. In ban da a baya-bayan nan Falasɗinawa na amfani da duwatsu ne inda ’yan gwagwarmayar su na Hamas ke amfani da rokoki. A duk lokacin da irin wannan yaƙi ya ɓarke ’yan Hamas su ka tava Yahudawa biyu ko uku, sojojin Isra’ila kan kwaso jiragen yaƙi su yi ta ruwan boma-bomai a kan musamman zirin Gaza.

Duk mai binciken lamuran tsaro ya san labarin hukumar leƙen asiri ta Isra’ila wato MOSSAD ta na daga mafiya ƙarfi a duniya a jerin irin CIA ta Amurka da KGB ta Rasha. Don haka ba yadda za a kamanta qarfin Falasɗinawa da Yahudawan Isra’ila. Abun da ma ya kan kawo jan zaren yaƙin shi ne Falasɗinawa da dama sun zaɓi gwagwarmaya da kasadar rabuwa da ran su fiye da zama a gida su jira dirar bom. Yara ƙanana na Falasɗinawa kan tashi su na jin ƙarar bindigogi da boma-bomai da ma shawagin jiragen yaƙi.

Yaron da ya taso a irin wannan yanayi zai iya zama marar fargaba fiye da wanda ya taso a sassan duniyar da ganin jami’an tsaro ma kusan sai a akwatin talabijin. Siyasar duniya ta zama tsakanin masu ƙarfi da raunana. Hakanan da ƙasashen da ke dogaro da goyon bayan manyan ƙasashe masu ƙarfin makamai don ba su kariya. Irin waɗannan ƙasashe na tsakiya wato su ba masu ƙarfin makamai ba kuma su ba matalauta ba kan zama sun fi maida hankalin yadda shugabancin su zai dore don haka kai tsaye su kan yi takatsantsan wajen marawa raunanan ƙasashe baya ga muradun da su ka sabawa manyan ƙasashen da ke kare su.

Irin wannan yanayi ke kawo cikas ga zaman lafiya ko samun kafa ƙasar Falasɗinawa mai ’yanci. Isra’ila kuma da ke da mara bayan mafi ƙarfin ƙasashe a duniya kan iya take dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya da sunan kare kan ta. In mu ka duba Isra’ila, kusan ta na zagaye ne da ƙasashen Larabawa amma za a iya cewa duk in sun taru a ƙarfin makamai ba za a iya cimma ƙarfin Isra’ila ba. A na da tabbacin Isra’ila na da makaman ƙare dangi. Tarihi ma ya nuna yadda yaqin kwana 6 a 1967 tsakanin Isra’ila da ƙasashen Larabawa ya kasance.

Ƙasar Isra’ila a lokacin ta na ma ƙarƙashin tasirin Firaminista mace ta farko wato Golda Meir da ta zama Firaminista a 1969 ta yi galaba mai tsanani a kan ƙasashen Larabawa har ma ta kwace wasu sassa na ƙasar Sham wajen tuddan Golan da har yanzu na hannun Isra’ila. Bayanai sun nuna Isra’ila na da muradin cigaba da faɗaɗa ƙasar ta. Don haka kwace sauran yankunan Falasɗinawa ba abun mamaki ba ne. Tambaya a nan ina ’yanci ko adalci a duniya?

Isra’ila ta kai mummunan hari kan wani asibiti ana yankin Gaza inda ta yi kisan gilla ga majinyata da sauran Falasɗinawa waɗanda su ka fake kimanin 500.

Harin na ruwan boma-bomai ya faɗa kan asibitin Al-Ahli Al-Arabi da ke cikin zirin Gaza.

Wannan shi ne mafi munin zubar da jinin hari a lokaci ɗaya da sojojin Isra’ila su ka kai kan Gaza tun wani hari ƙetaren iyaka da ‘yan Hamas su ka kai cikin Isra’ila.

Ƙasashen Larabawa, Turkiyya da Iran sun yi Allah wadai da wannan hari da buƙatar dakatar da kisan gilla kan fararen hula. Kuma a gaskiya kusan iya gudunmawar zahiri da Larabawa za su iya yi wa ’yan uwan na su kenan a yankin Falasɗinu. In an duba duk ƙasashen Larabawa masu ƙarfi na da alaƙa mai girma da manyan ƙasashen yammacin duniya da ke marawa ƙarfafar Isra’ila da mara mata baya.

Haƙiƙa wannan yanayin da a ke ciki na da alaƙa da siyasar duniya da kuma muardun kowace ƙasa daga cikin ƙasashen. Indai Allah wadai na amfani kan Isra’ila da tuni ƙasar ta wargaje. Ba ma tunanin wargajewa a ke yi wa Isra’ila ba a’a ta ma amince da barin Falasɗinawa su kafa ƙasa da ke maƙwabtaka da ita mai cikekken ’yanci. An yi yarjejeniyoyi da taruka masu yawa a baya amma sai lamarin ya zama kan takarda ko muhawara a kafafen labaru.

Firaministan Falasɗinawa Muhammad Shtayyeh ya zayyana harin da kare dangi ga Falasɗinawa kuma duk ƙasashen da ke marawa Isra’ila kan wannan yaƙi na da hannu ko haƙƙi a kisan.

Harin na zuwa ne yayin da shugaban Amurka Joe Biden ke shirin ziyartar Isra’ila don mara mata ma ta baya kan yaƙin ta da Hamas.

Alamu na nuna wannan ba yaƙi ba ne da zai ƙare nan take in an duba shirin gwamnatin Isra’ila ta Benjamin Netanyahu na kai hare-hare ta ƙasa.

Zuwa yanzu fiye da Falasɗinawa miliyan 1 suka ƙauracewa gidajen su daga yankin Gaza don gujewa barazanar kawo hari ta ƙasa kan yankin.

Isra’ila ta buƙaci dukkan fararen hula su fice daga yankin Gaza don shirin kawowa ’yan Hamas gagarumin hari.

Tun harin ba za ta da ’yan Hamas su ka kai kan Israila ta hanyar keta shingen tsaro mai tsaurin gaske, sojojin Isra’ila su ka yi ta ruwan wuta kan Gaza har su ka kashe fiye da mutum 3,300 akasarin su fararen hula.

Saudiyya a na ta bangaren na tuntuvar qasashen duniya don neman dakatar da zubar da jinin fararen hula a yaƙin na Hamas da Yahudawa.

Limaman masallatan jumma’a a sassan Nijeriya sun yi huɗubar Juma’a inda su ka marawa gwagwarmayar Falasɗinawa baya kan faɗa da su ke yi yanzu da ƙasar Isra’ila.

A nan malaman na nuna an daɗe a na cin zarafin Falasɗinawa ba tare da manyan ƙasashen duniya sun ɗau matakin kare su ba.

Hakanan limaman sun buƙaci a cigaba da addu’ar kawo ƙarshen fitinar da kuma yi wa Falasɗinawa fatar samun nasarar kafa ƙasa mai ‘yanci.

A masallatan salloli 5 ma na wuni, an samu waɗanda su ka ƙara addu’ar Alƙunut don samun maslaha a lamarin da ya jawo zubar da jinin jama’a ciki da mata da ƙananan yara.

Da Alamun Isra’ila Na Shirin Kai Hari Ta Ƙasa A Kan Gaza;

Da alamun sojojin Isra’ila na da niyyar kai hari ta ƙasa yayin da a yanzu haka su ke ta jefa boma-bomai a kan Gaza.

Kakakin Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Stephane Dujarric ya bayyana labarin umurnin da Isra’ila ta bayar na mazauna yankin arewacin Gaza da su ka kai miliyan 1.1 su ƙaura daga yankin.

Dujarric ya ce, hakan ba abu ne mai yiwuwa ba don haka majalisar ta buƙaci karin haske daga Isra’ila don fahimtar muradin ta kan neman tashin Falasɗinawa daga yankin arewacin Gaza.

Tuni shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas ya nuna sam bai amince da tashin Falasɗinawa daga yankin arewacin Gaza ba don hakan tamkar NAKBA ne da a ka yi da ya ke nufin yadda a ka tilasta Falasɗinawa 760,000 su ka bar gidajen su 1948 daidai lokacin da a ka kafa ƙasar Isra’ila.

Ministan wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya tattauna ta wayar tarho da ministan wajen Sin Wang Yi kan batun ruwan wuta da Yahudawa ke yi kan Gaza.

Yarima bin Farhan ya nuna buƙatar dakatar da zubar da jinin farar hula a kowane ɓangare da bin dokokin duniya a yanayin yaƙi.

Hakanan Saudiyya ta buƙaci Sin a mtsayin ta na mai kujerar dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, ta yi amfani da matsayin ta wajen dakatar da wannan farmaki kan Gaza.

A halin yanzu dai kayan tallafi sun isa ƙasar Masar don yunƙurin shigar da su Gaza inda jama’a da su ka maƙale ke matuƙar buƙatar su.

Kammalawa;

Ido ya koma kan Amurka, Turai da ma Rasha wajen kawar da siyasar muradu zuwa dakatar da zubar da jinin waɗanda ba su yi wa kowa laifi a Gaza ba. Kazalika ko don wanke Majalisar Ɗinkin Duniya daga zargin zama ‘yar amshin shatar ƙasashe masu nukiliya; ya dace a koma teburin shawari don kafa ƙasar Falasɗinu mai helkwata a gabashin birnin Kudus. Ga ƙasashen Afurka da ma Nijeriya ya na da kyau a taya raunana a Falasɗinu da mara baya da addu’a maimakon bugewa da ɗora laifi ko ɓarkewa da muhawara mai zafi da juna kan dacewa ko rashin dacewar bin kadun Falasɗinawan.

Kazalika kushe Falasɗinawa da nuna ‘yan Hamas ne su ka zunguro Isra’ila ba lallai haka ba ne don kusan kullum Falasɗinawa na cikin barazanar kisa ne ta dalilan da ke da ban mamaki kamar zargi kawai na wani daga cikin su na da alamun kai hari. A tarihi bakin bindiga kan kashe rayuka amma ba ya iya kashe kishi ko imanin da ke cikin zukata.