Gwamnatin Tarayya ta ba da wa’adin shekaru biyar ga shigo da alkama Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Ministan harkar noma da kiwo na Nijeriya, Abubakar Kyari, ya ba da wa’adin shekaru biyar ga Nijeriya ta daina shigo da alkama daga ƙasar waje. A cewarsa, hakan yana lamushe tanadin kuɗin wajen da Nijeriya ta yi.

Kyari ya yi wannan bayani ne ga ‘yan jaridu jim kaɗan bayan ya duba ingancin irin shukar alkama a Kano ranar Juma’ar da ta gabata.

A cewar sa, ya gamsu da cewa, samar da abu a cikin ƙasa shi ne ƙashin bayan noma. Kuma a cewar sa, gwamnati tana ta ƙoƙari wajen ganin an daina shigo da tsabar alkama ƙasar nan nan da shekaru huɗu zuwa 5.

Ministan ya ƙara da cewa, gwamnatin tarayya ta samar da tsare-tsaren ba da tallafin kaso 50 ga manoman alkama a wannan ranin mai zuwa don tabbatar da an samu alkama mai yawa a ƙasar.

A cewar sa, wannan yana daga cikin ƙudure-ƙuduren Shugaba Bola Ahmad Tinubu na ganin ya wadata ƙasar Nijeriya da isasshen abinci. Wannan ya sa ma ya yi kira ga jihohi a kam su samar da gonakin noma alkama don noma.

Ƙasar Jigawa ita ta fara nuna sha’awa sosai har ta ba da filin noma mai girman hekta 40,000 don noman alkama. Wannan ya kusa kai wa hektoci 70,000 da gwamnatin tarayya ta ware don ta cimma a wannan shekarar.

A cewar sa, idan an cimma wannan burin na gwamnatin Tarayya, to zancen shigo da alkama zai zama tarihi a Nijeriya.