Bankin Fidelity ya dakatar da tura kuɗi ta Opay da sauransu

Daga AMINA YUSUF ALI

Bankin kasuwanci na Nijeriya, Bankin Fidelity ya toshe ƙananan bankuna kamar OPay, Palmpay, Kuda, da Moniepoint saboda rashin tantance masu ajiyarsu.

Rashin sanin masu ajiya KYC na waɗancan ƙananan bankuna ya fiye sako-sako abinda yake jawo matsalar zamba a bankuna. 

Wannan dalili ne ya sa banki na Fidelity ya toshe tiransifar kuɗi zuwa bankunan Moniepoint, Kuda, OPay, da PalmPay, a cewar wasu da suke da masaniya mai ƙarfi a kan lamarin. 

A satin da ya gabata ne dai wasu masu ajiya da bankin Fidelity suka lura da cewa, an cire sunayen waɗancan ƙananan bankuna daga cikin jerin bankunan da za a iya hulɗa da su a manhajar hada-hadar kuɗi ta Bankin Fidelity.

A ƙalla kuma majiya daban-daban har guda biyar sun tabbatar da hakan. 

Sai dai kuma wasu majiyoyi daga bankunan da aka toshe sun bayyana dalilin da ya sa sunayen bankunasu suka yi ɓatan dabo daga cikin jerin bankunan da suka cancanci a yi hulɗa da su a manhajar bankin da cewa tangarɗar na’ura ce wacce ake kan gyarawa. Duk kuwa da cewa har yanzu sunayen bankunan nasu sun yi batan dabo. 

Wasu shaidun gani da ido sun sanar wa da majiyarmu cewa, wannan takunkumin tiransifa da aka sa wa bankunan tun sati biyu da suka wuce ne. Saboda yawaitar samun kesa-kesai na zambar kuɗi da rashin tantance masu ajiya. 

Sai dai OPay ya musanta cewa wannan korar ta shafe shi.  Haka kuma ita ma Sofia Zab, Babbar jami’ar kasuwanci a Palmpay ta shaida wa majiyarmu cewa, bankin Fidelity ya ba su sanarwar suna gyara a shafinsu kuma za su dawo da su idan an kammala. Haka ma wata majiya a Moniepoint ma ya tabbatar da al’amarin. 

Sai dai kuma har yanzu Bankin Fidelity ya ƙi tofa albarkacin bakinsa a kan al’amarin. 

Sai dai wata majiya mai ƙarfi daga bankin ta tabbatar da cewa bankin ya ɗauki wannan mataki ne saboda yawan asara da ya sha tafkawa sakamakon zambar kuɗi da ta sha ritsawa da shi a dalilin sakaci da bayanan mutane masu ajiya a banki.