Ɗaura aure ba bisa ƙaida ba: Kotu ta aike da ango da amarya da waliyyansu zuwa gidan gyaran hali

Daga WAKILINMU

Kotun Shari’ar Musulunci dake zama a ƙofar fada a Haɗejia ƙarƙashin mai shari’a Aliyu Muhammad Kwalam ta soke wani aure da aka yi ba bisa ƙa’ida ba, inda ake zargin wani saurayi da budurwa sun ɗaura wa kan su.

Waɗanda ake tuhumar su 5 sun haɗa da Angon da Amarya da Waliyyansu da kuma mai masaukin baƙi.

A cewar ɗan sanda mai gabatar da ƙara sufeta Ya’u Ismail ana tuhumar aikata laifuka 3 da suka haɗa haɗin baki da tada hankalin jama’a laifin da ya saɓa wa sashen doka na 122.

Da kuma laifin karya dokar musulunci ta ɗaura aure ba tare da sanin magaba ta ba, da kuma laifin ɗaura aure ba tare da shaidar lafiya ba wanda gwamnatin jihar jigawa ta sanya a matsayin doka a ranar 27 ga watan oktoban 2018, a cewar kotu hakan ya saɓa da sashen dokar penal code na 92, da kuma laifin zuga da tayar da hankalin jama’a wanda ya ci karo da sashe na 288.

Waɗanda ake ƙarar sun haɗa Ango Yahya Isah da Amarya Sa’adatu Rabi’u da kuma wakilin ango Yakubu Yakson, da waliyyin amarya Usman Rabi’u, da kuma Adamu Abdullahi dake zama babban shaida kuma mai masaukin baƙi.

Waɗanda ake tuhumar sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa.

Kotun karkashin mai shari’a Aliyu Muhammad Kwalam ta aike dasu zuwa gidan ajiya da gyaran hali har zuwa ranar 1 ga watan nuwamba mai kamawa domin cigaba da saurarar ƙarar.

Babban limamin masaurautar Haɗeja Malam Yusuf Abdurrahman Ya’u ya nuna rashin jin daɗinsa kan abinda matasan suka aikata wanda suka fake da fatawarsa.