Ribar dimukraɗiyya sai hamdala a Zariya, amma a ƙara duba mata – Hajiya Salamatu

Daga ISAH GIDAN BAKKO a Zariya

Wata fitacciyar ‘yar siyasa a Jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar birnin Zariya, Hajiya Salamatu ta bayyana yadda wasu zaɓaɓɓu ke rabon ribar dimukuraɗiyya a gundumomi goma sha uku a ko ƙaramar hukumar Zariya sai dai ta koka na yadda mata ba a yayyafa masu kamar yadda ake yayyafa wa maza ba a cewarta.

Hajiya Salamatu ta ci gaba da cewa duk wani ɗan siyasa da kuma waɗanda ba ma siyasar suke yi ba, ya san jam’iyyar APC ta yi sa’ar samun wakilai guda biyu da suka san yadda al’umma suka yi amfani da damar da suka samu suka zaɓe su a kujeru daban-daban kuma a cewar ta, wasu daga cikin zaɓaɓbun suna bakin ƙoƙarinsu wajen wakilci nagari da kuma tallafa wa al’umma.

Hajiya Salamatu Hayatu ta bayar da misali da shugaban majalisar wakilai Dokta Abbas Tajuddeen na yadda ya fito da wasu tsare-tsare da ke tallafa wa matan aure da kuma waɗanda mazansu suka rasu.

Hajiya Salamatu ta kuma bayar da misali da ɗaan majalisar jihar Kaduna mai wakiltar birnin Zariya Barista Mahmud Lawal da ya tallafa wa mata da suke yin ƙananan sana’o’i kamar ƙosai alale da kunun tsamiya da dai sauran sana’o’i masu yawan gaske.

Akan haka Hajiya Salamatu Hayatu ta bayyanan ire-iren tallafin da al’umma ke gida na ci gaba da yin sana’o’in da za su tallafa al’umma.

Ta ci gaba da cewar in an duba gudunmuwar da mata da maza suka bayar tun daga lokutan yaƙin neman zaɓe ya zuwa lokacin zave mata na da kashi fiye da saba’in da biyar cikin ɗari duk wani nasara da jam’iyyar APC ta samu mata ne akan gaba na yaƙin neman zaɓe, ya zuwa samun nasarar zaɓen.

A kan haka sai Hajiya Salamatu ta yi kira ga duk wani ɗan siyasa da ke da halin son kai, da ya daina, domain hakan ba shi da amfani qwarai da gaske.

A ƙarshe Hajiya Salamatu Hayatu ta jawo hankalin waɗanda aka ba su ribar dimukuraɗiyya da su ƙara ba takwarorinsu su riƙa tallafa wa waɗanda layin bai kai inda suke ba.