Kamfanin NNPCL ya gargaɗi masu ɓoye man fetur

Daga AMINA YUSUF ALI

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, ya gargaɗi jama’ar ƙasar Nijeriya da su kiyayi sayen mai suna adanawa, don tsoron fuskantar ƙaranci da ƙarin farashin man.

Wannan gargaɗi ya biyo bayan ƙaruwar jerin motoci ne a gidajen mai a sassan ƙasar a ‘yan kwanakin nan.

NNPC, ya ce yin gargaɗin ya zama wajibi, bisa la’akari da yadda aka fara ganin layukan ababen hawa a gidajen mai a birnin Ikko, cibiyar kasuwancin ƙasar, da birnin tarayya Abuja da dai sauran wasu garuruwa na Nijeriyar.

Wata sanarwa da kamfanin man ya fitar, ta ba wa ‘yan Najeriya tabbaci, cewa an gano bakin zaren dangane da abin da ya haddasa layukan ababen hawa a gidajen man.