Na biya wa mutum shida Umara saboda murnar zagayowar Mauludin Manzon Rahama – Sharif Sidi Abdulkaqadir

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Alhaji Sharif Sidi Abdulqadir Sarkin Baƙi, Fitaccen sharifin nan wanda ke kashe miliyoyin nairori wajen tallafa wa maqota sama da 400 a abinci a duk wata da kuma yin hidima ta maqudan kuɗaɗe a wajen shirya katafaren Mauludi da kuma raba kuɗaɗe da kayayyaki da kujerun Makkah duk shekara.

Ya ce wannan karon ya biya wa muta ne biyar waɗanda suka samu cin gasa da yake shiryawa a duk Maulidi na waɗanda suka sa wani suna ko dai sunan da ya dace da sunayen iyalan gidan Manzon Allah ko kuma sunayen da ya dace da sunayen gidan ahlin ma’aikin Allah, alaihimun salatu wasalam, inda a wannan shekarar ta 1445 hijirar ma’aikin Allah daga Makkah zuwa Madina sharun ya biya wa mutane biyar wanda su ka ci wannan gasa ta hanyar sunansu ya dace da yadda Sharif Sidi Abdulqadir Sarkin Baqi ya ke nema na sharaɗin cin gasar da kuma bada kyaututuka a wannan Mauludi na bana.

Daga cikin waɗanda suka samu kujerar ummarar, akwai mai suna Ali, sai kuma mai suna Fatima, waɗanda dukaninsu sunaye ne na ahlin Manzon Allah ahlil baiti da suka fito daga gida ɗaya kamar yadda sharaɗin gasar yake sai kuma fito ne daga gida guda a matsayin sharaɗin cin wannan gasa wanda Sidi Abdulqadir ya ke shiryawa duk shekara.

Haka kuma akwai mai suna mai ɗakin Manzon ta farko Khadija, sai kuma mai suna Muhammad, sai kuma Abu Ɗalib mai sunan Baffan Manzon Allah wanda waɗanan sunaye da suka fito daga gida guda sune suka samu kyautar maƙudan kuɗaɗe da kayayyaki da buhunan shinkafa sai kuma kujerar Ummara kowannensu a yayin da shi Abi Ɗalib bayan kujerar ummara harma da mashin Lifan sabo fil a leda, sai kuma ta cikon shidan wacce zata jagoranci wannan ummara da ikon Allah ita ce mahaifiyar Sidi Abdulqadir Sarkin Baƙi, kamar dai yadda ya bayyana a jawabin da ya gabatar a wajen gagarumun wannan maulidi da yake shiryawa duk shekara a kano, inda ya ce yaso ya biya musu kujerar Makkah ne amma saboda yanayin shekara ga abinda ya samu.

A ƙarshe ya ce yana fatan waɗanan masu zuwa ummara za su isar da saƙo da ƙara jaddada salati ga ma’aikin Allah, da kuma tabbatar cewa Sidi yana tare da kakansa da ahlinsa da kuma kasancewarsa na damuwa da rashin sanin inda zai ziyarci kabarin ɗiyar ma’aikin Allah, ya kuma yi kira ga al’uma na su haxa kansu wajen kaunar juna da aiki na gari domun dacewa a duniya da lahira, malamai da dama ‘yan kasuwa da shugabani da ‘yan makaranta da sauran al’umma suka halarci wannan Mauludi da kuma samun kyautar girmamawa daga Sarkin Baƙi.