Daga JAMIL GULA a Kebbi
‘Yan kasuwa da ke hada-hada kan hanyar garin Bachaka da ke kan iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar a ɓangaren Jihar Kebbi sun koka bisa yadda jami’an tsaro suka mayar da su waɗansu shanun tatsa.
Alhaji Umar Ɗankirya ɗaya daga cikin shugabannin ‘yan kasuwa da ke sayar da abinci ne ya bayyana haka a wata zantawa da wakilinmu a garin Bachaka ƙarshen makon da ya gabata.
Alhaji Umar ya ce jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda da masu hana fasakwabri da jami’an shige da fice da na farin kaya da ke aiki kan wannan hanyar suna daga cikin waɗanda ke ta’azzara tsadar kayan masarufi musamman kayan abinci saboda daga garin Bachaka zuwa Argungu akwai shingen bincinke aƙalla arba’in da bakwai na jami’an daban-daban kuma kowane sai ya ƙayyade kuɗin da za a ba su.
Sun mayar da wannan hanyar wajen tatsar kuɗi daga hannun ‘yan kasuwa kamar mu ba ‘yan Nijeriya ba ne, inji shi.
Ya ƙara da cewa su fa kasuwanci su ke yi saboda haka ba za su yarda su faɗi ba sai dai su ƙarawa kayan tsada ta yadda za su dawo da kuɗaɗen kuma su ci riba wanda a ƙarshe zai ƙare a kan talakawan da ke sayen kayan abinci hannunsu.
Ya kira ga shugabannin da wannan lamarin ya shafa tun kama daga sarakuna zuwa hukumomin gwamnati da su ɗauki matakin kawo canji saboda idan ba haka ba za su kashe waɗannan kasuwanni dake kan iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar ko kuma a samu matsala tsakanin jami’an tsaron da ‘yan kasuwa.
