Tare da BASHIR MUDI YAKASAI
Batunmu na wannan makon shine, hasken rana da kuma iska a matsayin sinadiran da za su samar da makamashi da zai samar da wutar lantarki ga gidajenmu da ofisoshinmu da guraren gudanar da sana’oi da suke buƙatar wutar lantarki har da masana’antu da suke buƙatar wutar lantarki har da masana’antu da kamfanoni da gonaki, kai da duk wuni guri da ake buƙatar wutar lantarki.
Kimiya, wato Ilimin ƙwaƙwa da na ci da kuma zurfafa tunani kan al’amari mai tafiya da kuma komowa, sai kuma ilimin fasaha wato, ilimin sarrafa abubuwa zuwa wani abun. Ɗan Adam ya fara bayyana a doran ƙasa sama da shekaru 5,400,000 da suka shuɗe, amma a ƙididdiga ta malaman tarihi na Islama mutane irinmu, wato bil adama, wato ’ya’ya da jikoki na Annabi Adamu (AS) da matarsa Nana Hauwa’u ba su wuce shekaru 152,000 ba.
’Ya’ya waɗannan bayin Allah su ne suke da wannan ƙwaƙwa-kimiya da fasaha suka shiga bincike da nazarce-nazarce, tun daga abinci ta tsinkar ’ya’yan itatuwa har suka gano yadda ake suka abincin irin na ƙarƙashin qasa irin su doya, rogo, makani, gwaza da na gida da na daji da kuma tsintsaye.
Bil adama ya fi duk wata halitta da ke doran ƙasa basira da hikima da kuma wayo kuma ya sarrafa su zuwa wani abu da zai amfane shi ta fannin tattalin arziki da siyasa da kuma zamantakewa Bil-Adama ya karade duniya kuma ya zauna a dukkan Nahiyoyin nan, ya shiga ƙarƙashin ƙasa ya fito da ƙarafa daban daban kamar azurfa da tagulla da tama da kuza da zinariya da lu’u-lu’u da kuma murjani har da makamashin kwal da man fetur da gas da kuma ‘uranium’ da kuma sarrafa ruwan kogi, wato ‘hydroelectric power’.
Wata hikimar da ɗan adam yake bibiya ita ce yadda ake sarrafa hasken rana da kuma iska. Ita rana tana ɗaya daga cikin Taurari da suke sararin subuhana da suke unguwa-unguwa. A unguwar Rana a kwai wasu halittun da masu nazarin sararin samaniya wadanda suke tare da wannan duniya ta Bil-Adama su Tarene da a kwai Mercury, Venus, sai wannan duniya ta mu wato Earth, sai mar, sai kuma Jupiter da Saturn da Uranus da Neptune da kuma Pluto.
Daga wannan duniya ta mu ta Bil-Adama zuwa Rana ya kai tsohon kilo mita 149,600,000, wannan tauraro rana ita ce ta fi kusa da mu, idan aka kwatanta da sauran biliyoyin taurari da suke sararin samaniya kamar yadda muka zaiyana kuma ta aiko mana da tsirrai da dabbobi da tsintsaye da kwari. Malaman Falaqi sun tabbatar mana cewa, wannan duniyar tamu ta wuce shekaru biliyan 15.
Wannan ba wai Allah na aiko mana da makamshi wato, ‘energy’ duk minti takwas zuwa wannan doro na duniya, musamman ma ƙasashe da muke tsakiyar duniya, wato ekwaita (equator) duk tsahon awa 12. Hikima da fikira ta ɗan adam yana iya sarrafa wannan makamashi zuwa ‘solar energy’ da wannan makamshi za mu iya dukkan wani al’amara da muke buƙatar wutar lantarki.
Bari mu ba da misalai da Nijeriya da za su mayar da hankali wajan amfani da ‘solar energy’, wato makamashin sola da ’yan Nijeriya za su rage kasha 95% cikin 100 na kuɗaɗensu a sha’anin girke-girke, domin kuwa ba sa buƙatar makamashin kwal ko gawayi ko itace ko gas ɗin dirki ko kanazir ko kuma wutar lantarki daga NEPA.
’Yan Nijeriya na shan wuya ne saboda hukumomi sun ki yarda Nijeriya ta mayar da hankali wajen samar da wutar solar, hasken rana, domin kuwa rana kyauta ce daga Allah, amma an ki gwadawa ‘yan Nijeriya da sauran ƙasashe masu tasowa kamar makotan mu jamhuriyar Nijar da Benin da Togo da Ghana da Burkina faso da ke cikin majalisar Ɗinkin Duniya, ba don komai ba sai don sun mayar da duniya mai bin aƙidar jari hujja.
Siyasar duniya ta a tara kudi ga ’yan ƙalilan mutane da za a riqa kiran su ‘Millionaires/ Millionairess’, wato mace da ta yi kuɗi da za ta ɗauki Dalar Amurka milliyan guda ta tafi shan iska a bakin tekunan duniya kamar sauda beach da ke Philippines da a ƙasar Tanzaniya ga kuma wajen kashe kuɗi, don kawai ka sha iskar teku ka kuma taka yashi mai laushi kamar kuncin jaririn da aka Haifa kwana daya, kamar Hnalei Bay da ke Hawai a ƙasar Amurka.
Ɗan uwana ko kuma na ce, ‘yar uwata mai karatu duniya cike take da mutane masu kayshi da wawura da Babakere da kuma Handama amma saboda halin bayar da wannan makamshi shi ya sa ya boye fasahar da kimiyar wajan samar da makamshi ya rike man fetur wanda sai an yi dawainiya mai yawa kafin makamshin ya samu, kuma sai yaga dama zai sa farashin da za a biya shi kafin ka amfana.
Farashin shi zai tsara duk wani farashi na abinci magani na karatun ‘ya’yan mu da mahallin da zamu sanya hakarkarin mu kan shin fuda da zamu huta idan mun dawo daga kodago. Idan muka kula da amfanin iska wajan samar da makamshi da za ayi amfani da fasahar da take tattare da ‘Wind Energy’ da duniya ta yi sallama da yunwa da fatara da Talauci da kuma faɗace-faɗace har da yake-yake a tsakanin ƙasashe, duk rashin tsaro da ya sha kan shugabannin wannan ƙasa shi ne dogaro da kafa guda ɗaya wajan samar da makamashi domin rayu, domin kuwa kowa akwai a gidan sa.
‘Wind Energy,’ ko kuma ‘wind power’ fasaha ce ta amfani da inji Turbin (turbine), wata na’ura ce da take da ikon ɗaukar karfin da iska ke da shi wajan samar da wutar lantarki a lokacin da ruwan wuƙaƙe (blades) ta kada su zuwa gurun da samar da wutar a tara ta kuma a rarrabata zuwa ga mabuƙata.
Wani abin sha’awa ga hanyar samar da wutar lantarki da iska suna da yawa masu farfela guda uku kamar yadda muke gani a jiragen sama da ake kira ‘Horizontal-Axis Turbines da kuma ‘Vertical- Axis Turbiness, wato dai masu farfela tsaye da kuma kwance, sai wadanda ba sa buƙatar iska mai yawa, ana kiranta da ‘utility-scale ‘wind.’ Sai kuma wanda ake yin su a cikin Teku-‘Offshore wind.’
Ida nana maganar alfanu na makamashi daga iska, shi samar da aikin yi domin duk masu ƙananan sana’oi, misali shagunan Teloli da Gidajen Abinci da Shagunan Aski da Kwalliyar mata da Tukubar masu Tsire da Balangu da Kantunan sayar kayan kwalam da maƙulashe da gidajen silima da filin Dambe da kokawa da kuma Gidan Gala, Mganar gaskiya duk wata karamar sana’a ‘wind Power’ zai bunƙasa wannan ƙaramar sana’ar. Baya ga haka makamashi daga iska ba shi da wani hadari kamar yadda man Fetur da Gas suke da shi, kuma makamashi daga iska shine da karkara.
Lokaci yayi a Nijeriya da duk wani ilimi na kimiya da fasaha da zai bunƙasa harkokin rayuwa misali a kiwon lafiya da samar da makamshi daga Rana da Iska da Shara a fara koyar da shi da harshen Uwa kamar Hausa da Yarabanci da kuma yaran Ibo- Iyamuranci, Ilimin zai Bunkasa cikin kankanin lokaci wannan za ta fita daga ƙangin rashin wuta, saboda haka sana’oi za su bunƙasa kamar yadda muke gani a indiya da malaysiya da indonesiya da koriya ta arewa da kuma japan.
In dai Jamus da Faransa da Potugal da ita kanta Uwar gijiyarmu zasu yi ilimin su da harshen ƙasar su kuma babu abin da sa kerawa a fannin kimiya da fasaha bamu ga dalili ba da munyi ililmi da harshen wasu mazalinta kuma ɓarayi lokaci ya yi da za mu ce ba mu yarda ba, mu haɗu a mako mai zuwa.
