Mahimmancin rubuta bayanan kasuwanci

Daga ZAUREN TASKAR NASABA

Bayanan Kasuwanci (Record keeping) ‘yan kasuwa masu yawa suna buƙatar ƙara sanin taskacewa ko rubuta bayanan kasuwanci abu ne mai matuƙar mahimmanci da kawo cigaban kasuwancin. Sai dai wasu cikin ‘yan kasuwa basu ɗauki rubutun bayanan kasuwanci a matsayin abu mai amfani ba, don haka ba ruwansu da shi.

Misali za ka samu ɗan kasuwa ya sayo atamfa a Kano a kan kuɗi N 9,000 ya ɗauke ta zuwa Adamawa ya sayar a kan Naira 9,500 yana tunanin ya ci ribar N500 wanda a zahiri haka ne, ya samu ribar N500.

Amma ɗan kasuwa wanda yake kiyaye rubutu ya san cewa idan yana so samun ribar N500 to fa ba zai sayar da wannan atampa ba a kan Naira 9500 har sai ya rubuta dukkan lissafin ɗawainiyar da aka yi mata daga Kano zuwa Adamawa kamar su kuɗin mota, abinci, masauki, kati, da duk wani abu da ya kashe ya fitar da ribar shi a rubuce sannan ya sayar da ita kuma ya aje wannan rubutu domin anfanin gaba.

Rubutu a bayanan kasuwanci yana bawa ɗan kasuwa damar sanin wane kayane mutane suka fi saya, wannene baya tafiya.

Yana taimakawa ɗan kasuwa wajen tsara yadda zai gudanar da kasuwanci nan gaba.

Kuma yana kuma ba da daman sanin adadin riba da yake samu a cikin sati, wata ko kuma shekara.

Rubutu a bayanin kasuwanci na ba ma ɗan kasuwa damar sanin ƙarfin jarinsa.

Da yawan bankuna ko kuma hukumomi dake ba da tallafi ko kuma bashin havaka kasuwanci, suna buqatar rubutun da ɗan kasuwa ya yi a kundin kasuwancinsa, wani lokaci domin tabbatar da inganci da tafiyar kasuwancin.

Yin rubutu a kasuwanci na ba wa ɗan kasuwa damar ajiye bayanan abokan cinikayya domin sake ƙulla alaƙar kasuwanci da su a gaba.

Taskance bayanan kasuwanci a rubuce na bama ɗan kasuwa damar ajiye bayanan ‘yan bashi.

Hakan yana ba ɗan kasuwa damar ɗaukan matakan gaggawa a duk lokacin da wata matsala ta ɓullo cikin kasuwancinsa. Amfanin rubutu ga kasuwanci suna da yawa za mu ci gaba da kawosu a jerin rubutun mu masu zuwa.

Wasu daga cikin hanyoyin adana bayanai.

Hanyoyin sun danganta da irin kasuwancinka.

  1. Za ka iya amfani da manhajar Microsoft Excel a computer ko waya ka dinga ƙididdige adadin kaya da kuɗin da suka shiga ko suka fita a shagonka tare da sauran bayanai na bashi, riba ko kuma faɗuwa.

2- Ɗan kasuwa na iya yin amfani da manhajar ‘inventory management system’ domin ajiye bayanai na duk abubuwan da suka shafi kasuwancin sa.

  1. Rubutawa a littafin na musamman wanda aka ware domin taskace bayanan kasuwanci.
  2. Za ka iya tattara rasitai na kayayyakin da ka siyo ka riƙa lissafa su kamar bayan sati ko wata ɗaya da sauransu sannan kuma kana adana su don anfanin gaba. Duk tsarin da ka zaɓa ya kasance zai biya buƙatarka na sanin yadda kasuwancinka ke tafiya.

Ƙarin Bayani: Kowani aiki kake yi ana buƙatar adana bayanai na kasuwancinka sabida hakan zai taimaka wa gwamnatin wajen yin dokoki da kare muradin ‘yan kasuwa, hakan zai ƙarfafa guiwar masu zuba jari ko taimaka maka wajen kasuwancin ka, kuma zai kare ka daga yawan tafka asara da ɗaukan darasi don ki yaye makomar kasuwancin ka ko cinikayya.