Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar APM kan ƙalubalantar nasarar Tinubu

Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da Jam’iyyar Allied People’s Movement (APM) ta shigar inda take ƙalubalantar nasarar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaɓen 2023.

A ranar Litinin Kotun ta yi watsi da ƙarar bayan da mai ƙarar ta janye ƙarar da ta ɗaukaka.

APM ta ɗaukaka ƙarar ne don ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023 wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Tun da fari, Jam’iyyar ta AMP ta nuna rashin gamsuwarta da hukuncin Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yanke wanda hakan ya sa ta sake shigar da ƙarar tata a kotu ta gaba.

Matakin janye ƙararta da APM ta yi na nufin kotu ta yi watsi da ƙarar ke nan.