Jaruma Tonto Dikeh ta sauya sheƙa zuwa APC

Jaruma a masana’antar Nollywood wadda ta tsunduma harkar siyasa, Tonto Dikeh, ta sauya sheƙa ta koma Jam’iyya mai mulki ta APC.

Jarumar ta koma APC ne bayan da ta fice daga Jam’iyyar hamayya ta African Democratic Congress (ADC).

Jarumar ta yi takarar mataimakin gwamna ƙarƙashin ADC yayin zaɓen 2023 a Jihar Ribas.

A wannan Litinin ɗin ake sa ran Shugabar Matan APC ta Ƙasa, Dr Mary Alile, za ta karɓi Tonto Dikeh a Sakatariyar APC da ke Abuja da misalin ƙarfe 3 na rana.

A shekarun baya-bayan nan, an ga yadda jaruman fina-finai na Arewaci da Kudancin Nijeriya suka ba da himma wajen shiga harkar siyasa don a dama da su.