Janairun baɗi za a fara bai wa ɗalibai bashi a Nijeriya – Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa, ya zuwa watan Janairun 2024 shirinsa na bai wa ɗalibai bashi zai kankama.

Ya bayyana haka ne sa’ilin da yake jawabi a wajen taron tattalin arziki na ƙasa na 2023 ranar Litinin a Abuja.

“Ya zuwa Janairun 2024, sabon shirin bai wa ɗalibai bashi zai fara aiki. Don haka muke cewa babu sauran tafiya yajin aiki a rayuwar ‘ya’yanmu kuma ɗalibai a nan gaba,” in ji Tinubu.

A ranar bikin “June 12” Shugaba Tinubu ya sanya wa ƙudirin bai wa ɗalibai bashi hannu ya zama doka, alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓensa.

Kakakin Majalisa Wakilai a majalisa ta 9 kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a yanzu, Femi Gbajabiamila ne ya gabatar da ƙudirin domin bai wa ‘yan ƙasa samu zarafi zurfafa karatu cikin sauƙi.