Nijeriya ta gurfanar da Shugaban Kamfanin Binance a kotu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta gurfanar da kamfanin Binance Holdings Limited da manyan jami’anta biyu, Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla da ya gudu a gaban kotu bisa zargin ƙin biyan haraji.

An gurfanar da kamfanin da shugabannin biyu a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhumar Tigran Gambaryan ya isa kotun ne da misalin qarfe 9:15 na safiyar ranar Alhamis yayin da abokin aikinsa, Anjarwalla ba ya nan saboda an ce yana gudu.

Waɗanda ake tuhumar dai suna fuskantar tuhume-tuhume biyar na halasta kuɗaɗen haram, da kuma gudanar da sana’o’i na musamman a Nijeriya ba tare da lasisi ba.

A cikin ƙarar mai alama: FHC/ABJ/CR/115/2024, an zargi Binance da gaza yin rajista tare da hukumar FIRS don biyan duk harajin da ya dace da ayyukan su.

An ɗage cigaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 19 ga watan Afrilu sakamakon gazawar hukumar ta FIRS wajen bayar da shaidar tuhume-tuhume a hannun EFCC.